Yadda za ku kawar da kaushi da faso a ƙafafunku
A yayin da lokacin hunturu ya shigo arewacin Nigeria, a kan samu kaɗawar iska da ƙura da yanayin hazo wadda ke haifar da saurin bushewar fata tare da haddasa kaushi ko faso a ƙafafun wasu mutanen.
Ga hanyoyin da za ku bi domin ganin kaushi da faso basu ci mutuncin kafafun ku ba a lokacin wannan sanyi:
Wanke Kafa A lokacin Wanka:
Wannan shine mataki na farko na hana kafa tara datti da zai iya juyewa ya koma kaushi wanda daga baya ya ke tsagewar da ake kira da ‘faso’. A daure a ware lokaci domin wanke dattin tafin kafa duk lokacin da aka yi wanka. Za a iya amfani da sabulu da abin goge kafa da aka zaba.
A Shafe Kafa Da Mai:
Bayan an fito daga wanka, a shafe tafin kafa da saman kafa da man shafawa mai kauri musamman wanda ya kunshi man kadanya, ‘glycerin’, ko sinadarin ‘Vitamin A’ da ‘Vitamin E’.
A Ke Jika Kafa:
Ga wadanda fatar kafar su ke da karfi, za su iya jika kafar su a cikin ruwa mai dumi da aka zubawa gishirin kunshi ko wasu mayuka na musamman da ake samu daga fure (essential oils). Hakan zai sa kafa ta yi laushin da za a iya cire datti cikin sauƙi.
A Sille Kafa: A yi amfani da dutsen goge kafa ko soson wanke kafa na musamman wajen sille kafa a hankali. Yin hakan sau daya zuwa biyu a cikin sati zai hana kafa yin kaushi ko faso.
Amfani Da Suturar Rufe Kafa:
Suturta kafa ta hanyar yin amfani da takalmi kafa ciki ko kuma saka sutura, kamar safa, yayin amfani da takalmi mai sahu a waje/bude zai bada gudunmawa wajen hana kaushi da faso.
KU KUMA KARANTA: Rashin abinci mai gina jiki na barazana ga miliyoyin yara a Afrika.
Aiki Na Musamman:
Ga ma su son samun sakamako cikin gaggawa ko wadan da matsalar bushewar kafa ta saka a gaba, su na iya samun sutura ta musamman da ake sakawa da daddare kafin a kwanta. A wanke kafa tare da shafe ta da mayuka kafin a saka suturar lokacin da za a kwanta bacci.
Yawan Shan Ruwa:
A ke yawan shan ruwa domin tabbatar da cewa jiki bai shiga halin kishin ruwa ba. Isashen ruwa a jiki ya na taimakawa wajen inganta lafiyar fata.
A Nemi Shawarar Kwararru:
Ga wanda matsalar bushewar fata, kaushi, ko faso su ka gundura, sai ya hanzarta ziyartar cibiyar kula da lafiya mafi kusa don ganawa da kwararru da za su bashi shawara.