Yadda wata mace ta fille kan jaririnta da adda

1
228

Daga Maryam SULAIMAN, Abuja

Rundunar ‘yan sandan Kuros Riba ta tabbatar da kama wata mata da ta fille kan yaronta mai watanni 11, a unguwar Yonen da ke Ugep a karamar hukumar Yakurr ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Irene Ugbo ne ya tabbatar da faruwan hakan a ranar Laraba.

Ya ce an kashe yaron ne a ranar Talata, kuma nan take ‘yan sanda suka shiga domin hana daukar mataki kan matar..

KU KUMA KARANTA:Abinda ya sa aka janye dokar hana ‘yan adaidaita hawa manyyan tituna a Kano

Ugbo ya ce za a mayar da shari’ar daga Ugep zuwa sashin binciken manyyan oaifuka rundunar domin gudanar da bincike mai inganci.

Kakakin ya ƙara da cewa, “Abin takaici ne, kuma tuni ta na tsare a hannun jami’an tsaro, amma tabbas za a kai lamarin Kalaba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya tattaro cewa mahaifiyar ‘ya’ya biyu da ake zargin ta yi amfani da adda wajen yanke kan jaririn nata

Wani shaidan gani da ido ya ce, dan matar mai shekaru 8 ne, ya zo wurin kuma ya yi ihu, wanda ya ja hankalin makwabta.

Sai dai kuma shiga tsakani da ‘yan sandan suka yi a kan lokaci, inda nan take suka tsare matar a hannun jami’an tsaro, tare da fitar da ita daga garin Ugep, inda suka kubutar da ita daga wasu da suka fusata suka yi yunkurin far mata.

A halin da ake ciki, Obol Lopon na Ugep kuma mai mulkin Yakurr, Obol Ofem-Ubana Eteng, ya yi kira da a kwantar da hankula yayin da ‘yan sanda ke binciken lamarin.

“Nan da nan na kira taro da al’ummata domin duk da cewa abin da ya faru ya ɓata ƙasar, sai na tabbatar an kawo karshen zubar da jini.

“Mun yi kira kai tsaye ga matasa a Ugep da su san hanyar zaman lafiya da tunani a kan wannan danyen aikin kuma sun amince.

“Muna cikin kaɗuwa, amma mun samu nutsuwa kuma mun bar wannan al’amari a hannun ‘yan sanda.

“Ina tabbatar muku cewa ba za a ɗauki matakin ramuwar gayya ba saboda dole ne mu kasance masu bin doka da oda”, in ji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply