Connect with us

Kudanci

Yadda wani mutum ya kashe matar sa saboda burodi

Published

on

Wani magidanci mai suna Ndubisi Uwadiegwu ɗan jihar Enugu ya lakaɗawa matarsa ​​Ogochukwu Enene dukan tsiya har tamutu akan biredi.

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta fito daga ƙauyen Umuokpu, Awka, jihar Anambra, amma ta auri mijinta wanda ɗan asalin jihar Enugu ne.

Rahotanni sun nuna cewa ɗa na farko ga marigayiyar, mai shekaru 14, ya ce mahaifinsu ya lakaɗawa wa mahaifiyarsu duka ne lamarin da yayi sanadiyar mutuwarta, saboda ta nemi ya saya musu biredi amma ya ce ba shi da kuɗi.

Ɗan nata ya ƙara da cewa mahaifiyarsa ta yanke shawarar yin amfani da kuɗinta ta siyo wa yaran biredi ɗaya, amma mahaifin ya shiga kicin ya cinye biredin, da mahaifiyarsu ta tambaye shi dalilin da ya sa ya cinye wannan biredi, sai ya fara dukanta har abin ya kai ga mutuwarta.

Ko da yake har yanzu iyalan mamacin ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, amma wata majiya ta kusa da dangin ta tabbatarda aukuwar lamarin wanda ya faru a Legas.

Hatsari

Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗo a Legas

Published

on

Wani jirgin sama mai sauƙar ungulu ya yi hatsari a yankin Ikeja da ke Jihar Legas a kudancin Najeriya.

Wani jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta Legas ya ce jirgin ya kama da wuta jim kaɗan bayan rikitowarsa da tsakar ranar Talata a kusa da filin jirgin sama na Murtala Muhammad.

KALLI CIKAKKEN BIDIYON ANAN:

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, ‘National Emergency Management Agency’ (NEMA), ta ce mutum huɗu ne ke cikin jirgin kuma an ceto su da ransu.
Jami’in NEMA mai kula da sashen kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, ya ce ba su kai ga gano mamallakin jirgin ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Lamarin ya faru ne shekara uku bayan wani jirgin Helikwafta mallakar kamfanin Quorom Aviation ya faɗo a yankin Opebi na Legas ɗin a watan Agustan 2020.

Continue Reading

'Yansanda

Da wane dalili ‘yan sanda suka lakaɗa wa ɗan Okada duka a Legas?

Published

on

Wani ɗan Okada, mai suna Alasan Usman matashi mai ƙoƙarin neman na kansa domin rufawa kansa da ‘yan uwansa asiri.

A ranar jumu’a ‘yan sanda a jihar Legas suka tare shi suka ce ya kawo babur ɗinsa duk da dai bai san laifin da ya aikata ba, sai ya ƙi ya basu. Saboda ya ƙi basu suka masa duka sai kace ɓarawo sai da suka yi masa jina-jina yadda ba zai iya taɓuka komai ba, sannan suka tafi da mashin ɗinsa.

KU KUMA KARANTA: Ranar zuma ta duniya: Amfani da sirrikan dake tattare da zuma

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan Arewa mazauna Legas sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin an baiwa wannan ɗan Okada haƙƙinsa.

Yanzu haka shugaban hukumar ‘yan sanda na jihar Legas ya ziyarce shi a inda yake jinya, sannan an mayar masa da kuɗin belin da aka karɓa na mashin ɗinsa an kuma ba shi guduwmawa mai yawan gaske, kuma yana nan yanzu haka yana samun sauƙi sosai a unguwar Abbatuwa dake Legas.

Continue Reading

Hatsari

Fashewar bututun ɗanyen mai yayi sanadiyar mutuwar mutane 12

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da cewa mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar magudanar mai a safiyar Juma’a a yankin Rumuekpe da ke ƙaramar hukumar Emoha a jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, inda ta ce shaidar farko ya nuna waɗanda abin ya shafa na ɗiban ɗanyen man ne a lokacin da wurin ya kama wuta.

KU KUMA KARANTA: Kwastam ta kama tramadol ɗin naira miliyan 306 a Kaduna

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa, hakan ya afku ne a yayin da wata motar bas ɗauke da ɗanyen mai ta kama wuta, yayin da take barin wurin zuwa wata matatar mai ta haramtacciyar hanya a yankin.

“Ya zuwa yanzu mutane 12 ana kyautata zaton sun ƙone kurmus. Har yanzu ba a gama sanin sunayen waɗanda abin ya shafa ba,” inji ta.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like