Yadda Melaye, da wasu ‘yan jam’iyya suka fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓe a fusace

2
392

Wakilin jam’iyyar PDP na ƙasa, Dino Melaye da wasu wakilan jam’iyya sun fice daga babban ɗakin taro na ƙasa da kasa da ke Abuja bisa zargin maguɗin zabe.

Dino wanda ya fice daga wurin taron a Litinin, ya yi zargin cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta yi ƙasa a gwiwa tare da tafka maguɗin zabe don jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress ta lashe zaɓe.

KU KUMA KARANTA: Yadda Peter Obi ya doke Tinubu a Legas

Ya ce, “Bayan lura da cewa shugaban hukumar ta INEC ya ƙudiri aniyar yin maguɗin zaɓe ta hanyar tabbatar da cewa ba a saka sakamakon zaɓe ba, ta hanyar yin barazana da maida mu mutanen banza wanda basu san me suke ba, to muna nan ne don mu murƙishe maguɗin da aka tsara tsakanin INEC da jam’iyyar APC.

Mu ‘yan Najeriya ne. Babu wani wuri da aka aka ɗora sakamakon.

“Jam’iyyun siyasa a nan sun fito ne don nuna rashin jin daɗin yadda aka sanya siyasa da son zuciya a tsarin zaɓenmu.” Injishi.

2 COMMENTS

Leave a Reply