Yadda Malam Ibrahim Shekarau ya lashe kujerar sanata a ƙarƙashin NNPP

0
393

Hukumar zaɓe ta INEC ta ayyana Malam Ibrahim Shekarau jigo a jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya a shekarar 2023 a ƙarkashin jam’iyyar NNPP

Shekarau, Sanata ne mai ci a NNPP kuma an tsayar da shi takarar kujerar Sanata a karkashinta. Sai dai kafin zaɓe ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP tare da yin watsi da burinsa na Sanata bayan ya koma PDP.

Sai dai daga baya Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta dage cewa har yanzu ta amince da shi a matsayin halastaccen ɗan takarar jam’iyyar NNPP, duk da cewa jam’iyyar ta maye gurbinsa da wani ɗan takara mai suna Rufa’i Sani Hanga.

KU KUMA KARANTA: Yadda Melaye, da wasu ‘yan jam’iyya suka fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓe a fusace

Shekarau, wanda zai je zauren majalisar a karo na biyu, an bayyana hakan ne ta bakin jami’in zaɓe na mazaɓar Sanata, Farfesa Tijjani Hassan Darma.

A cewar INEC, Shekarau ya samu kuri’u 456,787 inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Abdulkarim Abdussalam Zaura, wanda ya samu kuri’u 168, 677.

Leave a Reply