Yadda kotu a Kano ta aike da jarumar tiktok, Murja Kunya gidan yari

0
310

Wata kotu a Kano ta aike da Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan gyaran halinka. Murja dai ta shahara musamman a shafin tiktok wurin yin bidiyo.

Tun da farko dai lauyan gwamnati Barrista Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata tuhume-tuhumen da ake zarginta da su inda Aisha Najamu da Idris Mai Wushirya suka kai ƙararta, suka ce ta yi bidiyo wanda ta ci zarafinsu a shafin na tiktok.

Bayan karanto mata wannan zargin Murja ta musanta hakan. An kuma tuhume ta a karo na biyu wadda wani lauya Barrista Ali Hamza ya gabatar inda aka zarge ta da yaɗa kalamai na batsa da shiga ta batsa da yunƙurin tayar da hankalin al’ummar jihar Kano.

Lauyan Murja Barrista Zaharadeen ya nemi kotu ta bayar da belinta inda har ya yi roƙo kan a mayar da wannan lamari zuwa hukumar Hisbah amma kotu ba ta amince ba.Kotun ta ɗage zaman shari’ar zuwa 16 ga watan Fabrairun 2023. domin cigaba da sauraron ƙarar.

Leave a Reply