Connect with us

Sojoji

Yadda jana’izar sojojin rundunar da ke kare shugaban ƙasa da aka kashe a Abuja ta kasance

Published

on

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta binne sojoji biyar da ke rundunar kare shugaban ƙasa waɗanda ‘yan bindiga suka kashe a kwanakin baya.

An binne sojojin ne a maƙabartar Guards Brigade da ke Maitama , Abuja, a cewar sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Godfrey Anebi Abakpa. Cikin waɗanda aka binne har da Kyaftin Attah Samuel.

Yayinda ake bankwana dasu

“Kafin rasuwarsu, sojojin suna aiki a Bataliya ta 7 da ke barikin Lungi da ke Maitama da Bataliya ta 176 da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja,” a cewar sanarwar.

Shugaban rundunar Laftanar Kanar Salim Yusuf Hassan ya bayyana Kyaftin din da kuma sauran sojojin a matsayin kwararru a fanninsu kuma sun jajirce wajen kare martabar Najeriya.

A watan jiya ne wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojojin kwanton-bauna a yankin Bwari da ke Abuja inda suka kashe su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Sojoji

Kwamandan mayaƙan Boko Haram da wasu mutum 5 sun miƙa wuya ga sojoji a Borno

Published

on

Kwamandan mayaƙan Boko Haram da wasu mutum 5 sun miƙa wuya ga sojoji a Borno

Masu tada ƙayar bayan sun yi watsi da ayyukan ta’addanci tare da miƙa wuya ga sojojin ne a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki.

Mayaƙan Boko Haram 6 ciki har da kwamandan ‘yan ta’adda sun miƙa wuya ga dakarun Rundunar MNJTF, ta haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, babban jami’in yaɗa labaran rundunar ta MNJTF, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya bayyana sunan kwamandan ‘yan ta’addar da Adamu Muhammad.

Ya kuma zayyano sunayen sauran ‘yan ta’addar da Isah Ali mai shekaru 18 da Hassan Modu ɗan shekara 18 da Nasir Idris mai shekaru 23 dogarin kwamanda Jubilaram, Usman Rash da Abba Aji mai shekaru 21 da kuma Abubakar Isah ɗan shekara 20.

A cewar sanarwar, “‘yan ta’addar sun tsere daga maɓoyar tsagin ISWAP dake Jubilaram, dake shiyar kudancin tafkin Chadi.

KU KUMA KARANTA:Shugaban sojojin Isra’ila ya amince da shirin kai hari a Rafah

Adamu mai shekaru 22, ya taka rawa a hare-hare da dama da aka kai kuma ya karaɗe garuruwan Kangarwa da Alagarno da Doro Naira da Dogon Chikwu dake ƙaramar ƙungiyar hukumar Kukawa ta jihar Borno”.

A cewar kakakin Rundunar ta MNJTF, fiye da ‘yan ta’adda 100 ne suka tuba tun bayan da aka ƙaddamar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsaftace yankin tafkin Chadi mai laƙabin “Operation Lake Sanity” a turance wanda manufarsa ita ce kakkaɓe masu tada ƙayar baya daga yankin.

Yace tun daga ranar 23 ga watan afrilun da ya gabata, masu tada ƙayar baya 119 ne suka miƙa wuya tare da yin ƙira ga takwarorinsu su rungumi tafarkin zaman lafiya tare da ajiye makamai.

Continue Reading

Sojoji

An harbe kwamandan sojoji a Katsina

Published

on

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Ɗan’Ali a ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan-ɓauna da aka kai musu.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis kuma an ajiye gawar marigayin, mai muƙamin Manjo a wani asibiti a Katsina.

an yi wa kwamandan kwanton-ɓauna ne a ƙauyen Malali da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, inda aka ƙira shi da ya ƙaro sojoji domin daƙile harin da aka kai ƙauyen.

KU KUMA KARANTA:Zulum ya buƙaci Sojoji su samar da sansani a dajin Sambisa

“Kamar yadda kuka sani Malali na kan titin Zangon Pawwa, kuma yankin gaba ɗaya ‘yan bindiga sun ƙwace. A duk lokacin da aka kai hari jami’an tsaro sukan nemi a kawo musu ɗauki daga sansanin Maraban Ɗan’Ali, kuma wannan sabon kwamandan zai mayar da martani cikin gaggawa.

“A wannan karon sun nemi a ƙara masa jami’an soji, ya zo ne da wata mota ƙirar Hilux, maimakon tankar yaƙi, wataƙil tamkar ba ta samu ba a lokacin. Abin takaicin shi ne kawai sai maharan da suka kai masa hari, sun harbi motar sannan shima su ka harbe shi a ka.”

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa, a yayin da ake ƙoƙarin ɗauko gawarsa daga wurin da lamarin ya faru, an yi artabu da muggan makamai tsakanin ‘yan bindigar da jami’an soji, inda jami’in da ya ɗauko gawar shi ma ya samu rauni na harbin bindiga.

Continue Reading

Labarai

Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindigar da suka addabi Birnin Gwari

Published

on

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe wasu ƴan bindiga da suka addabi yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna a arewacin ƙasar.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai riƙon muƙamin mataimakin mai magana da yawunta, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar ranar Alhamis da maraice.

Laftanar Kanar Yahaya ya ce dakarun nasu sun kuma kuɓutar da mutane da dama da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.

“Dakarun Runduna ta 1 ta Rundunar Sojin Najeriya da ke sintiri a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ranar 6 ga watan Fabrairun 2024 ta gamu da ƴan bindiga. Yayin da suke gumurzu, dakarun sun kawar da ƴan bindiga huɗu amma wasu sun tsere da raunukan bindiga,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: An samu arangama tsakanin sojoji da wasu mutane a Mangu da ke Filato

Ta ƙara da cewa ta ƙwato makamai da suka haɗa da bindigogi da alburusai da babura da ƴan bindiga ke amfani da su wurin kai hare-hare.

Haka kuma rundunar ta ce ranar 7 ga watan nan dakarunta sun samu bayanan sirri na ƴan bindiga da suka sace wasu mutane a ƙauyen Kwaga na Birnin Gwari inda suka yi musu dirar mikiya lamarin da ya sa suka tsere.

Dakarun sun kuɓutar da mutum goma sha ɗaya da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su, a cewar Laftanar Kanar Yahaya.

Yankin na Birnin Gwari na cikin wuraren da ƴan bindiga suke yawan kai wa hare-hare inda suke kashe mutane sannan su yi garkuwa da wasu. Sai dai a baya bayan nan rundunar sojin Najeriya ta ce ta zage dantse wajen magance matsalar.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like