Yadda gobara ta yi ɓarna a ƙauyukan Jigawa

Wata gobara ta laƙume ƙauyukan Malamawar Dangoli, Karangi, da Kwalele da ke ƙaramar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa, inda ta lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.

Gobarar wacce ta tashi a ranar lahadin da ta gabata, ta ci gidaje, da dabbobi, da kayayyakin gona, da sauran kayayyaki masu daraja, sai dai an yi sa’a, ba a sami asarar rayuka ba, amma rahotanni sun ce wasu mutane sun ɓace.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: APC ta bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga waɗanda bala’in gobara ya rutsa da su a kasuwar Maiduguri

Sanarwar ta kara da cewa, “Babu asarar rayuka da aka samu kawo yanzu, amma wasu daga cikin ‘yan uwa da ake zargin sun yi gudun hijira sun bace.”

Tawagar ‘yan kwana-kwana da ‘yan sanda daga jahohi, tarayya, da ma’aikatan kashe gobara sun isa wurin domin dakile gobarar.

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Ibrahim Abdullahi Gumel, ya ɗora alhakin gobarar akan wasu itatuwa da aka ƙone waɗanda ba a san suwa suka ajjiyesu a kauyukan ba.

Ya shawarci jama’a da su guji ƙona ciyayi da ke kusa da kauyuka a lokacin damina.

“Muna ƙira ga mutane da su yi taka-tsan-tsan da gobara tare da guje wa ƙona ciyayi da wuraren sharar gida ko gona a cikin ko kusa da kauyukansu,” in ji shi.

Mutanen ƙauyen da abin ya shafa yanzu suna ƙidayar asarar da suka yi, saboda gobarar ta cinye duk abin da tayi karo da shi.

Lamarin dai ya jefa iyalai da dama cikin ruɗani da rashin matsuguni, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin gobarar, hukumomi na tunatar da mazauna garin da su yi taka tsantsan don hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

A halin da ake ciki, Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Jigawa, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara ne a sakamakon iska mai karfin gaske da ta dauko gobarar daga murhu na dafa abinci.

Ya ce gobarar ta tashi daga gida gida inda suka yi asarar kadarori da dama da kuma kayan abinci da ke ajiye a rumbu. “Duk da haka, ni tare da mataimakin gwamnan muna kan hanyar zuwa kauyuka kuma za mu ba su abinci, tufafi, da barguna a matsayin kayan agaji,” in ji shi.


Comments

One response to “Yadda gobara ta yi ɓarna a ƙauyukan Jigawa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda gobara ta yi ɓarna a ƙauyukan Jigawa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *