Yadda direban mota ya mutu a layin manfetir

0
337

Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba, ya mutu a lokacin da yake ƙoƙarin sayen manfetir a layin gidan mai a ya kin Oluyole, da ke ƙaramar hukumar Oluyole ta jihar Oyo.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, kuma a lokacin da lamarin ya faru, babu wanda ya san cewa mutumin da ya ɗora kansa a kan sitiyarin motarsa ya rasu har sai da wasu kwastomomin suka danna hon motar su, don sanar da shi ya yi gaba, ashe ya mutu.

Motar mamacin mai lamba AKD 878 GP, an kai ta ofishin ‘yan sanda mafi kusa, yayin da aka ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar a wani asibiti.

KU KUMA KARANTA:Mutuwar ma’aikaciya NTA a hatsarin Jirgin ƙasa: Rashin bin ƙa’idar hanyar jirgin ne- NRC

Wata majiya ta ce, “har yanzu ba a san ko wanene mutumin ba, mamacin ya rasu ne yana zaune a cikin motarsa ​​da kafarsa ɗaya akan feda, ɗaya kuma a kasa lokacin da aka bude kofar motar”

Manajan gidan man, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, waɗanda suka ɗauke gawar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, bai amsa wayarsu ba, a lokacin da wakilinmu yayi ƙoƙarin jin ta bakinsa.

Leave a Reply