A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamban 2022, jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wani mutum mai suna Ganiyu Shina mai shekaru 49 da ke No 4, Oguji Street, Obantoko a Abeokuta, bisa zarginsa da laifin yin wanka da jini a wani kogi da ke unguwar kotopo a ƙaramar hukumar Odeda.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi ya sanya wa hannu, an kama wanda ake zargin ne a lokacin da jama’ar yankin suka gan shi a bakin kogi, inda ya ajiye motarsa kirar Nissan, ya fito da wani soso na gargajiya da wata roba da ke cike da jini, ya fara wanka dashi.
“Nan da nan ya gano cewa wasu mutane suna kallonsa, sai ya fara gudu amma jama’ar unguwar suka bi shi suka kama shi.
“Shugaban al’ummar yankin ne ya ankarar da ‘yan sandan da ke sashin Aregbe, inda nan take DPO, SP Bunmi Asogbon ya jagoranci tawagar ‘yan sintiri zuwa wurin, inda aka kawo wanda ake zargin ofishin ‘yan sanda.
“Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa yana da matsalar aljanu, kuma wani boka ne ya umarce shi da ya yi wanka da jinin, ya ce jinin da ke hannunsa ba na mutum ba ne, na saniya ne.” Inji shi.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a ɗauki sauran jinin domin bincike a ɗakin gwaje-gwaje, domin sanin ko jinin mutum ne ko a’a.
Kwamishinan ya kuma yabawa al’ummar yankin da rashin daukar doka a hannunsu, don haka ya basu tabbacin za a binciki wanda ake zargin yadda ya kamata.