Connect with us

Doka

Yadda aka kama Mr 442 da abokinsa da takardun bogi a Nijar

Published

on

Hukumomin ƙasar jamhuriyar Nijar sun ce sun fara bincike kan yadda mawaƙan nan biyu ‘yan Najeriya suka mallaki takardun bogi na ƙasar.

Zuwa yanzu mahukuntan ƙasar Nijar na ci gaba da tsare Mubarak Abdulkareem wanda aka fi sani da 442 da manajansa Orler of Kano a gidan yarin birnin Yamai inda suke zaman jiran kammala bincike kamar yadda babban mai shigar da ƙara na gwamnati ya shaida wa manema labarai.

Babban mai shigar da ƙara a ƙasar ya ce babban laifi ne yin amfani da takardun bogi a jamhuriyar Nijar , ya ƙara da cewa sun bayar da umarni a gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin gaskiya game da lamarin.

Ya ce ”Duk wanda aka samu da laifi za mu tasa ƙeyarsa zuwa gaban kotu, ba za mu yadda wasu su riƙa amfani da takardun ƙasarmu ta hanya wadda take ba ta gaskiya ba, kuma nan gaba duk wanda aka kama da irin wannan laifin to ya kuka da kanshi”.

A ɗaya ɓangaren ƙungiyoyi masu yaƙin kare haƙƙin bil adama sun fara kiraye-kirayen a bincika domin gano yadda aka yi mawaƙan suka samo takardun zama ‘yan ƙasar, kasancewar sun samo takardun ne a wasu wuraren kafin su zo wajen da za a yi musu fasfo, tare da kiran a yi musu adalci.

Babban mai shigar da ƙarar ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ana neman belinsu kan sefa (CFA) ta Nijar miliyan 10, ya ce har yanzu babu wata takarda da ke nuna hakan, kuma a cewar sa idan ma ta zo, to hakan ba zai taɓa tabbata ba sai da amincewarsa ko akasin haka.

1 Comment

1 Comment

  1. barszbee

    November 27, 2022 at 10:23 am

    Su cigaba da rike su kawai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Doka

Kotu ta umarci jihar Ondo da ta biya diyyar naira miliyan 30 ga mutumin da ‘yan Amotekun suka harbe

Published

on

Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wata babbar kotun Ondo da ke zamanta a Akure, a ranar Larabar da ta gabata ta umarci gwamnatin jihar Ondo da ta biya wani Oluwasegun Oluwarotimi kuɗi naira miliyan 30 a matsayin diyyar harbin bindiga da ya samu a wata arangama da jami’an tsaro na jihar, wanda aka fi sani da ‘yan Amotekun.

Oluwarotimi mai shekaru 36, mai tuƙa babur ne, wato ɗan okada ne lokacin da lamarin ya faru.

A nasa jawabin, Mai shari’a Adejumo ya bayar da umarnin a biya Oluwarotimi kuɗi naira miliyan talatin a matsayin diyya.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NYSC ta biya diyya ga dangin ɗan bautar ƙasa da ya ɓata

Oluwarotimi, wanda a yanzu an yanke shi ne sakamakon harbin da aka yi masa ba bisa ka’ida ba,inda ya shigar da karar a gaban kotu.

“B bisa ka’ida ba a titin Araromi a ranar 9 ga watan Agustan 2021 a Akure, harbin da Amotekun ta yi ya saɓa wa hakkin ɗan Adam.

“Kotu ta umurci waɗanda ake ƙara da su hada kai su biya Naira miliyan 20 ga wanda ake kara a matsayin diyya na gaba daya da kuma Naira miliyan 10 a matsayin diyya ta misali,” in ji alkalin.

Continue Reading

Doka

An sanya dokar hana fita a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar ta-ɓaci har zuwa faɗuwar rana don kaucewa taɓarɓarewar doka da oda, biyo bayan tattara sakamakon zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin.

KU KUMA KARANTA: Yadda Abba Kabir Yusuf na NNPP ya lashe zaɓen Kano

Ya ce an yanke shawarar ne don hana ’yan daba su haifar da hargitsi a halin da ake ciki.

Kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su kasance a cikin gida domin jami’an tsaro ba za su ƙyale kowa ko wata ƙungiyar da ke da niyyar haddasa fitina ba.

Continue Reading

Doka

Kotu ta sanya sharudɗa akan batun bada belin doguwa

Published

on

sharudɗan sune kamar haka:

Kotu ta haramtawa Alhassan Ado Doguwa zuwa mazaɓarsa ranar zaɓen ta gwamna da ‘yan majalisar jiha.

Wannan dai na cikin sharudɗa da babbar kotun tarayya ta sanya kafin bada belin Alhassan Ado Doguwa.

Ga dai ƙarin jerin sharudɗan da kotu ta sanya kafin bada belin.

1- Zai ajiye zunzurutun kuɗi har naira miliyan 500

2- Gabatar da sarki mai daraja ta ɗaya a matsayin wanda zai tsaya mishi.

KU KUMA KARANTA: INEC ta cire sunan shugaban masu rinjaye, Doguwa daga jerin sunayen ‘yan majalisar wakilai

3- Gabatar da babban sakatare a gwamnatin jiha ko ta tarayya a matsayin wanda zai tsaya mishi.

4- Zai ajiye Fasfo da sauran dukkanin takaddunshi na tafiya a kotu.

A karshe kuma kotu tace bazai halacci mazaɓarsa ba yayin zaɓen gwamna da yan majalisun jiha dake tafe.

Ko ya kuke kallon wannan batu?

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like