Yadda aka gano gawar ɗan wasan ƙasar Ghana da girgizar ƙasa ta rutsa da shi a Turkiyya

1
362

An gano gawar tsohon ɗan wasan ƙasar Ghana, Christian Atsu bayan mummunar girgizar ƙasa da ta afku a ƙasar Turkiyya, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka rawaito a yau Asabar, suna nakalto manajansa.

Atsu, mai shekaru 31, girgizar ƙasa mai ƙarfi awo 7.8 da ta afku Turkiyya da Siriya a ranar 6 ga watan Fabrairu ta rutsa da shi, ta kuma kashe mutane fiye da dubu 43 a ƙasashen biyu.

Rahotannin farko sun nuna cewa an kuɓutar da tsohon ɗan wasan na Chelsea da Newcastle kwana guda bayan girgizar tkasar, amma daga baya aka gano ba ayi hakan ba.Manajansa a Turkiyya Murat Uzunmehmet ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na DHA a ranar Asabar cewa an gano gawarsa a ƙarƙashin baraguzan lardin Hatay da ke kudancin Turkiyya.

“Mun samu gawarsa babu rai. Ana ci gaba da kwashe kayansa. An kuma samu wayarsa,” Uzunmehmet ya fadawa DHA. Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Ghana ta ce ta samu “labari mara dadi”.

“Babban ɗan uwansa da tagwayen ‘yar uwar Christian Atsu da wani jami’in ofishin jakadancin Ghana sun kasance a wurin lokacin da aka tsinto gawar,” in ji ma’aikatar a cikin wata sanarwa. Ghana ta ce tana aiki tare da gwamnatin Turkiyya don shirya jigilar gawar zuwa ƙasar ta don binne gawar.

KU KUMA KARANTA: Ba za a manta da Pele ba, in ji hukumar kwallon kafa ta FIFA

Ɗan wasan tsakiya Atsu ya shafe shekaru huɗu a Chelsea kafin ya koma Newcastle na dindindin a shekarar 2017. Ya sanya hannu a watan Satumban da ya gabata a kungiyar Hatayspor ta Turkiyya Super Lig. Chelsea ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa, “Abin baƙin ciki ne da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta samu labarin cewa Christian Atsu yana ɗaya daga cikin wadanda bala’in girgizar ƙasa ya rutsa da su a Turkiyya da Siriya.

“Newcastle ta kuma ba da girmamawa ga “ɗan wasa mai hazaka kuma mutum na musamman”. Kulob ɗin ya ƙara da cewa, “’yan wasanmu da ma’aikatanmu da magoya bayanmu za su riƙa tunawa da shi a ko dayaushe.

“Da farko ya shigo kulob ɗin a ɗan aro, ya taka muhimmiyar rawa a cikin ‘yan wasan Magpies da suka sami nasarar lashe gasar Championship a 2017 kafin ya yi tafiya ta dindindin don taimaka mana mu kafa gurbinmu a gasar Premier.”

Ma’aikatan bincike da ceto sun gano gawar Atsu a inda yake zaune a Gidan Ronesans, wani katafaren gidaje na alfarma da ya ruguje a birnin Antakya da ke Hatay. ‘Yan sandan Turkiyya sun kama ɗan kwangilar ginin a filin jirgin saman Istanbul a makon da ya gabata a daidai lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Montenegro, a cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

1 COMMENT

Leave a Reply