Yadda aka fara gasar Alƙur’ani ta ƙasa karo na 38 a Yobe

0
182

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Musulmi su ci gaba da haɓɓaka gasar Gasar Karatun Al-ƙur’ani saboda yadda gasar ke ƙarfafa haddar Alƙur’ani a duniya baƙi ɗaya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi wannan ƙira ne a taron ƙaddamar da Musabaƙar Karatun Al-ƙur’ani ta Ƙasa Karo na 38 a Damaturu, Jihar Yobe.

Ya bayyana cewa gudanar da masabakar na haɓaka ilimin addinin Musulunci musamman a tsakanin matasa inda suke dagewa su karatunsa har su zama zakaru a duniyar Musulmi.

Sarkin Musulmi, wanda Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Ibn El-kanemi ya wakilta ya yaba wa gwamnatin Yobe bisa ɗaukar nauyi da kuma yadda aka raba ɓangaren maza da na mata wajen gudanar da gasar.

A jawabinsa na maraba a taron da ya gudana a Filin Wasa na 27 Augusta, shugaban kwamitin musabaƙar, tsohon gwamnan Yobe, Sanata Ibrahim Gaidam, ya yaba wa Jami’ar  Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato game da kokarinta wajen shirya gasar a matakin ƙasa.

Ya kuma jinjina wa kwamitocin gasar ta Alƙur’ani dangane da yadda suka jajirce wajen ganin an gudanar da shi, kamar yadda aka buƙata.

KU KUMA KARANTA: Madarasatu Nuruddeen Gudau, Ta Yaye Dalibai 41 Da Su Ka Yi Saukar Alkur’ani

Daga nan ya yi fatan kammala wannan gasa lafiya tare da neman cigaba da addu’ar neman zaman lafiya a duniyar musulmi da ma ƙasar mu ta Najeriya baƙi ɗaya.

Mataimakin shugaban jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Bilbis ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa ɗaukar nauyin gasar, da kuma yadda aka raba ɓangaren maza da na mata a wajen ƙaddamar da gasar.

Farfesa Lawan Bilbis ya ce mahaddatan da za su fafata a gasar da su kwantar da hankalinsu don ganin sun bi ka’idojin karatu kamar yadda Allah Ya shimfida, domin ta haka ne za su kai ga nasara.

A jawabinsa na buɗe gasar, Gwamna Mai Mala ya jaddada muhimmancinta ga al’ummar Musulmi saboda tana ƙarfafa musu gwiwa wajen meman ilimin addini da kuma sanin ka’idojin karatun Alƙur’ani.

Mai Mala ya buƙaci aiyaye da su haɗa hannu da gwamnati wajen fadakar da ‘yayansu game da muhimmancin zaman lafiya tsakanin da nisatar harkokin ta’addanci.

Ya ci gaba da cewar, a kwanakin baya majalisar dokokin jihar ta yi dokar kafa Hukumar Hisba wadda nan take aka amince da ita, kasancewar samar da hukumar ta Hisba zai taimaka wajen gyara tarbiyya musamman a tsakanin matasa.

Leave a Reply