Yadda ɗan damfara ya yaudari ’yan sandan Ngelzarma, da wasu mutane biyu: Labarin Bello Muhammad ​​da Sulaiman Garba

Bello Muhammad mazaunin garin Ngelzarma ne, a ƙaramar hukumar Fune ta jihar Yobe, Najeriya. Yana gudanar da sana’ar cajin waya, inda mutane ke kawo wayoyinsu ayi musu caji, kuma su biya shi kuɗin aikin sa.

Wani ɗan damfara ya zo shagonsa, sai ya ga wata waya mai tsada, sai ya yanke shawarar cewa sai ya mallaki wannan wayar, har da wasu wayoyinma. Kai tsaye ya nufi ofishin ‘yan sanda, da rigar ciki ta ‘yan sandan Najeriya, da katin shaida na ƙarya.

Ya gabatar da kansa a matsayin CID a hedkwatar, kuma ya ba da rahoton cewa ya bi diddigin wata wayar da aka sace (Tracking) zuwa wani wurin cajin waya, inda a take suka ba shi umarnin ya je ya kawo wayar, da kuma mai kula da shagon wayar. Don haka ya je shagon Muhammad Bello ya gaya masa irin labarin da ya faɗawa ‘yan sanda cewa ya bi diddigin wata waya da aka sata zuwa shagonsa, zai kai Muhammad ​​da wayar ofishin ‘yan sanda.

Muhammad da sanin cewa bai aikata komai ba, ya bishi har ofishin ‘yan sanda da ke bayan gari. ‘Yan sanda ba su ji ta bakin Muhammad ​​ba, suka cire masa kaya da ‘yan mukullinsa da wasu kayansa sannan suka kulle shi.

Muhammad Bello, mai shagon charjin waya

CID na bogi ya ɗauki wayar, da nufin fita daga ofishin ‘yan sandan, inda ya ba su lambar waya ta bogi tare da katin shaidar ƙarya. Da aka tambaye shi ko yana da wata shaida ta bin diddigin, (Tracking certificate), sai ya ce yana tare da sajan nasa a cikin gari, kuma zai je ya kawo.

Ya ɗauki babur ya wuce kai tsaye shagon Muhammad, ya umarci mai tsare shagon wayar daya kawo wayar maigidansa, suna kan binciken maigidan nasa ne a ofishin ‘yan sanda, aka aiko shi ya karɓi wayoyin.

Mai shagon ya gane mutumin a matsayin wanda suka fita tare da ubangidansa, ya fito da wayoyin Muhammad ​​guda biyu ya miƙa wa CID na bogi. Shi ko ɓarawo yaga ya mallaki wayoyin sata guda uku a hannunsa, sai ya arce.

A ofishin ’yan sanda kuwa, har kusan ƙarfe 3 na rana babu labarin CID da ya ce zai je ya dawo. Muhammad ya gaji, sai ya fara yin tambayoyi kamar haka ”ta yaya za a kama ni laifin da ban yi ba”,?
Abin da ban san komai game da shi ba?’

”Aikina shi ne cajin waya, babu ruwana da matsalar mallakin waya. Ina ganin ya kamata a yi cikakken bincike”.

Sulaiman Garba, wanda aka sace ma waya

”Mutumin da ya kawo wayar shagona ya kamata a yi ma tambayoyi, ba ni ba”. Inji Muhammad

‘Yan sandan sun amsa da cewa suna jiran CID ya dawo ne har yanzu. Muhammad ya ba da shawarar su ƙira shi ta waya, suka yi ta ƙira amma ba su samunsa, lambar bogi ce. Haka dai aka ci gaba da jira har ƙarfe biyar na yamma, a lokacin ne dangin Muhammad suka yanke shawarar ziyartar ‘yan sanda domin jin ba’asi.

Sun koka da yadda mutane ke jiran Muhammad a shagon domin karɓar wayoyinsu, don haka akwai buƙatar ‘yan sanda su sake shi. Sannan kuma sun yi tambaya game da inda CID yake, amma ‘yan sanda sun kasa yi musu cikakken bayani.

’Yan’uwan Muhammad ​​sun nuna rashin jin daɗinsu da jami’an da kawai suka yarda da wani labari daga wani baƙo ba tare da wata hujja ko shaida ba saboda ya zo da mari a hannun sa, da katin shaidar ƙarya.

Daga nan ne hankali ya fara tashi. ASP Musa Nuhu ya umarci Sajan da jami’an sa, da su je su nemo wannan CID ɗin a duk inda yake. Bayan sun shafe sa’o’i suna bincike, sai suka sanar da ɓacewarsa. ASP ya shaidawa Muhammad ​​cewa ”tare muka ganku, don haka babu abin da za mu iya yi”.

Ngelzarma chaji Ofis

Aka sallami muhammad, ya kai maganar wajen Lawani, inda Lawanin ya yi alƙawarin taimaka wa Muhammad. Sai dai abin takaicin shi ne, Lawanin bakinsu ɗaya da jami’an tsaro, don haka ya ƙira su, suka tabbatar da faruwar lamarin. Yayin da ya ke ƙiran ‘yan sanda, wasu ma’aurata da ke wurin kan batun aure sun ji shi a lokacin da ya ƙira ‘yan sanda.

Muhammad ​​ya ji ba a neme shi ba har an kwana, sai ya koma. Lawanin ya ce har yanzu bai gana da jami’an ba, don haka ya ƙara haƙuri. Muhammad ya koka da cewa mai wayar, mai suna Sulaiman Garba ya matsa masa sai ya biya shi wayarsa. “Na yi masa bayani cewa wayar tana wurin ‘yan sanda, amma yaƙi yarda da bayanina.”

Lawanin ya yi alƙawarin sasanta lamarin washegari. A washegarin, Lawanin Ya gana da ’yan sanda a cikin wani taron sirri, yayin da Muhammad ​​ke zaune a gindin wata bishiya a waje. Bayan sun tattauna ne suka yanke shawarar cewa Muhammad ​​ya kawo kuɗi su yi amfani da su wajen gano wayoyi ukun da aka sace.

Yanzu dai Muhammad yana cikin wani hali, ga ɓatan wayoyinsa, ga ɓatan wayar kwastomansa, a dalilin sakacin ’yan sanda.

Jaridar Neptune Prime ta ƙira PPRO na Damaturu, Dungus AbdulKareem don jin ta bakinsa, sai yace bai san komai ba game da lamarin. Bayan mun masa bayani, ya nuna rashin jin daɗin faruwar hakan, kuma ya umarce mu da mu bawa su Muhammad lambarsa nan take, domin ya taimaka musu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba mu san yadda ta ƙare ba tsakanin waɗanda abin ya shafa, PPRO, da kuma sashin ‘yan sanda na Ngelzarma.


Comments

One response to “Yadda ɗan damfara ya yaudari ’yan sandan Ngelzarma, da wasu mutane biyu: Labarin Bello Muhammad ​​da Sulaiman Garba”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *