A ranar alhamis ɗin da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta gurfanar da wani mutum mai suna Oni Samuel a gaban wata kotun majistare da ke zaune a Akure babban birnin jihar bisa zargin damfarar wata mata Blessing Olaitan kuɗi N120,000.
Tun farko dai jami’an hukumar sivil difens (NSCDC) na jihar sun kama Samuel bisa zargin aikata laifin a makon jiya.
A yayin da ake ci gaba da shari’ar, Olaitan ta shaida wa kotun cewa ita karuwa ce, inda ta ce wadda ake zargin ya karɓa mata kuɗi har naira dubu 80 bayan da ya yi lalata da ita a cikin wani dare mai cike da ƙaddara, inda ta bayyana cewa wadda ake ƙara ya yi alƙawarin miƙa mata kudin ta da kuma karin Naira dubu 15 ladan lalatar da yayi da ita, kuɗin karuwancinta.
KU KUMA KARANTA: Boka ya mutu a otal yana tsaka da lalata da matar fasto
Olaitan ta ce daga baya ta gano cewa sakon biyan kudin banki da ya turo mata na karya ne.
An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu da laifuka biyu da suka shafi haɗa baki da sata.
Takardar tuhumar ta ƙara da cewa, “Kai, Oni Samuel, da sauran jama’a a ranar 1 ga Maris, 2023 a Alagbaka, Akure da ke ƙarƙashin ikon wannan kotun mai girma, kun hada baki da kanka wajen aikata laifin, tare sace zunzurutun kuɗi har naira dubu ɗari da ashirin na Misis Blessing Olaitan inda ka aikata laifin da ya saɓawa sashe na 516 na kundin laifuffuka na doka Cap 37, Vol 1 na jihar Ondo,na shekarar 2006.
“Cewa, Oni Samuel a ranar 1 ga Maris din shekarar 2023 a Alagbaka, Akure da ke cikin ikon wannan kotun mai girma, ya saci kuɗi Naira dubu ɗari da ashirin na Misis Blessing Olaitan inda ya aikata laifin da ya saɓa wa sashi na 383 kuma hukuncin da za a yanke masa a ƙarƙashin sashe na 390 na kundin Code Cap 37, Vol 1 dokokin Jihar Ondo, 2006.”
Sai dai Samuel ya musanta zargin da ake masa, kuma lauyan da ke kare shi, Barista E.O Nifemi ya buƙaci kotun da ta bayar da belin wanda ake kara amma mai gabatar da ƙara na hukumar tsaro ta NSCDC, Mista David Ebriku ya ƙi amincewa da bukatar belin, inda ya roƙi kotu da ta ci gaba da tsare wanda ake ƙara.
“Idan wanda ake tuhuma ya sami beli, zai iya tsallake belin wanda zai iya zama haɗari ga al’umma”. In ji lauyan da ya gabatar da ƙarar
Da yake yanke hukunci a kan lamarin, Alkalin kotun, Tope Aladejana, ya bayar da belin wanda ake ƙara a kan kuɗi N200,000 tare da mutane biyu masu tsaya masa baki ɗaya sannan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 17 ga Afrilu, 2023 don cigaba da sauraren ƙarar.