Shahararren ɗan wasan barkwanci a yanar gizo, Abdulgafar Ahmad, wanda aka fi sani da Cute Abiola ya bayyana cewa rundunar sojin ruwan Najeriya ta amince da ficewar da yayi daga rundunar, domin ya mai da hankali sossai akan wasan barkwancinsa da ya sanya a gaba a yanar gizo.
Ɗan wasan barkwancin ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a shafinsa na Facebook, inda yace yin aikin sojan ruwa ya taimaka masa da horon da ake buƙata domin samun nasarar rayuwa.
“Tare da godiya mai zurfi, ina matukar godiya ga sojojin ruwa na Najeriya don ba ni wannan dama ta aiwatar da horon da ake buƙata don cigaban rayuwa, da kyawawan dabi’u, da kuma ɗa’a, kadan daga cikin alfanun da na samu a rundunar sojin ruwa.
“Samun horaswa a gurin ya nuna min cewa ba shakka ina da hankalin da ake buƙata domiin ci gaban ɗan adam, da kuma ci gaban rayuwa mai yalwa” inji shi.
A lokacin da yake godiya ga babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo da manyan takwarorinsa, ya yi kira ga magoya bayansa da su haɗa kai da shi wajen jajircewa domin bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasa sana’arsa ta wasan kwaikwayo.
“Ina kira ga ɗaukacin magoya bayana da su zo tare da ni wajen jinjina wa babban hafsan sojin ruwa da dukkan manyan abokan aikina da suka bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban sana’ata, yayin da na yi amfani da kafarsu wajen tabbatar da haƙƙina na kare kasarmu.
“Gaskiya, Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya ta zama taswirori na don samun ingantacciyar hanyar aiki.”
Ya ƙara da cewa, yadda babban hafsan hafsoshin sojin ruwa ya amince da ficewarsa daga aikin domin ya sami damar mai da hankali kan sana’arsa ta nishadantarwa, shaida ce da cewa rundunar sojin ruwa ta damu matuƙa da da buri da ma’aikatansu ke son cimma.
“Na yi mamaki game da amincewar ficewa ta daga Rundunar Sojan Ruwa da Babban Hafsan Sojan Ruwa ya yi don in sami isasshen lokacin da zan bi dom cika burina.
“Wannan aiki ɗaya tilo da babban hafsan hafsoshin sojan ruwa ya yi matuƙar birgewa kuma yana nuna yadda sojojin ruwan ke matuƙar sha’awar cika burin jami’ansu”
Cute Abiola ya bayyana cewa duk da cewa ya fice daga aikin sojan ruwa amma zai ci gaba da zama jakadansu nagari a gida da kuma ƙasashen waje.
“Har yanzu ina cikin dangin sojojin ruwa na Najeriya, kuma na yi alkawarin ci gaba da wakilci nagari a Najeriya ko a ƙasashen waje.
“Ina alfahari da na yi aiki a irin wannan rundunar sojojin ruwa ta Najeriya” inji shi
Ficewar sa daga Rundunar Sojan Ruwan na zuwa ne ‘yan sa’o’i kaɗan bayan Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara ya naɗa shi a matsayin mataimakinsa na musamman kan masana’antun ƙere-ƙere.
A watan Nuwamban shekarar 2021 ne rundunar sojin ruwan Najeriya ta tsare dan wasan barkwancin na wasu kwanaki a matsayin hukuncin da ya saɓa wa dokar soja ta hanyar sanya wani hoton bidiyo da yayi sanye da kayan soja a shafukan sada zumunta, lamarin da aka ce ya saɓa wa manufofin rundunar sojin Najeriya.