Waye Zai Lashe Zaben Cike Gurbi Na Majalisar Wakilai Ta Mazabar Jos Da Bassa?

0
599

Daga; Isah Ahmed, Jos.

A RANAR Asabar din mai zuwa ce, idan Allah ya kai mu, ake sa ran za a gudanar da zaben cike gurbi, na kujerar Majalisar wakilai ta tarayya ta Mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato.

Shi dai wannan zabe, za a gudanar da shi ne, sakamakon rasuwar Dan Majalisar da ke wakiltar wannan mazaba Marigayi Alhaji Haruna Mai-Tala, wanda ya rasu a daren ranar Juma’a 2 ga watan Afrilun, shekarar da ta gabata, a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi, a hanyar Abuja zuwa Jos.

Jam’iyyu 11 ne suka tsayar da ‘yan takara a wannan Zabe da za a gudanar, kamar yadda Hukumar zabe mai zaman kanta, ta Kasa INEC ta bayyana.

Hukumar zaben ta ce Jam’iyyun da suka tsayar da ‘yan takararsu, a wannan zabe da za a gudanar, sune APC da PDP da PRP da ADC da ADP da APM da APP da LP da NNPP da SDP da kuma YPP.

Ya zuwa wannan lokaci, wadannan ‘yan takara 11, da wadannan jam’iyyu suka tsayar a wannan zabe da za a gudanar, sun shiga kowanne lungu da sako na wannan mazava, sun tallata manufofinsu.

Amma masu nazarin harkokin siyasar wannan mazaba, na ganin wannan fafatawa zata fi yin zafi ne, tsakanin dan takarar APC Joseph Abbey da dan takarar PDP Musa Agah da kuma dan takarar PRP Gwani Muhammad Adam Alqali, wanda ya fice daga jam’iyyar APC, kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na wannan takara.

Ita dai wannan mazaba ta Jos ta Arewa da Bassa, tun daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2015, jam’iyyun adawa ne ke lashe zaven wannan mazava. Sai a zaben shekara ta 2015 da zaben shekara ta 2019 ne, jam’iyyar APC mai mulki a Jihar ta lashe Zaben.

Amma a wannan karon masu nazarin harkokin siyasar wannan mazaba, na ganin jam’iyyar APC mai mulki, zata iya fuskantar babban kalubale daga jam’iyyar PRP, musamman idan aka dubi yadda Jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda gwani na wannan takara, wanda ‘yan Jam’iyyar suka yi ta korafe korafe a kai.

Da dama daga cikin magoya bayan Jam’iyyar ta APC, sun zargi gwamnan jihar Filato Simon Lalong, da marawa Joseph Abbey baya kan wannan takara, a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na wannan jam’iyya. Don haka wasu suka rubuta takardun koke, kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin.

Har’ila yau masu nazarin harkokin siyasar, sun yi bayanin cewa babu tantama dan takarar APC na wannan zabe da za a gudanar, Joseph Abbey, wanda tsohon Kwamishinan harkokin kasuwanci da masana’antu ne na Jihar Filato, da ya fito daga yankin Rukuba da ke Karamar Hukumar Bassa. Zai kara samun cikakken goyan baya, daga gwamnan Jihar Simon Lalong, musamman idan aka dubi irin goyan bayan da ya bashi, a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar. Don haka suke ganin zai iya lashe wannan Zabe.

Masu lura da harkokin siyasar sun yi, bayanin cewa shima dan takarar jam’iyyar PDP Musa Agah, Dan Majalisar dokokin Jihar, mai wakiltar mazavar Irigwe da Bassa, da ya sauka. Wanda ya fito daga yankin Miango da ke Karamar Hukumar Bassa, zai iya samun dubban kuru’un magoya bayan jam’iyyar PDP na wannan mazaba, wadanda mai yiwuwa zasu kai shi ga iya lashe wannan zabe. Ganin cewa tun daga zaben shekara ta 2023, da suka rasa wannan kujera, ake fafatawa da su, a duk lokacin da aka zo, zaben wannan kujera.

Haka kuma masu hasashen na ganin shima dan takarar jam’iyyar PRP, Gwani Muhammad Adam Alkali, dan Siyasa kuma Dan kasuwa da ya fito daga Karamar Hukumar Jos ta Arewa, zai iya samun dubban kuri’un magoya bayan Jam’iyyar APC, da aka batawa rai a zaben fidda gwanin Jam’iyyar da zai kai shi ga lashe wannan Zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here