Waye zai ceci rayuwar Hauwa, yarinya ‘yar shekara 3

0
4
Waye zai ceci rayuwar Hauwa, yarinya 'yar shekara 3

Waye zai ceci rayuwar Hauwa, yarinya ‘yar shekara 3

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hauwa Adamu, yarinya ce ‘yar shekara 3 da rabi. Suna zaune a unguwar Tandari da ke cikin garin Potiskum jihar Yobe. Ita dai wannan yarinya tana fama da ciwo ne a cibiyarta, wanda ya kai wata uku tana fama da shi.

Mahaifiyar yarinyar ta ce, haka kawai suka wayi gari tana cewa cibiyarta tana mata ciwo. To sai suka je Asibitin ƙwararru da ke Potiskum, inda likitoci suka ce mata babu likitan da zai duba ta a nan, sai dai a je University of Maiduguri Teaching Hospital ko kuma Yobe State University Teaching Hospital Damaturu.

KU KUMA KARANTA:An sace wata dattijuwa a asibitin Dawanau dake Kano

To su kuma iyayen yarinyar ba su da kuɗin da za su je wadannan asibitin da aka ambata musu. Kullum ciwon ƙara ci gaba yake. Cibiyar ƙara kumbura take a duk wayewar gari. Kuma ga shi suna zaune a gida, ba a yi mata kowane irin magani, saboda ba su da kuɗi

.

Shi ne suke neman taimako a wajen al’umma domin a ceto rayuwar wannan yarinya.

Za a iya tuntubar wadannan numbers don jin halin da yarinyar take ciki da kuma taimakawa don a samu a kai ta Asibiti:
08148871924, 08025608283.

Leave a Reply