Wata mace ta mutu lokacin da jirgin ƙasa ya murkushe mota a Abuja

Jirgin ƙasa ya murƙushe wata mata da motarta yayin da take ƙoƙarin haye titin jirgin da ke unguwar Kubwa a Abuja ranar Alhamis.

Wani ganau mai suna Olisa Ogbechie, ya yi zargin cewa ‘yan sandan sun yi amfani da ƙarfi wajen fatattakar mutanen da ke son taimakawa daga wajen.

“A kokarin kubyutar da wanda abin ya rutsa da ita, da basu agajin farko da kuma ɗaukar yadda lamarin ya faru, ‘yan sandan da ke wurin suka hana ruwa gudu.

‘Yan sandan sun yi wa ni da wasu ‘yan tsiraru mummunan duka, yayin da suka yi ta harba barkonon tsohuwa a idona tare da wasu mutane biyu, sun nuna bindigogi yayin da suka tursasa mu barin wajen” inji shi.


Comments

3 responses to “Wata mace ta mutu lokacin da jirgin ƙasa ya murkushe mota a Abuja”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Wata mace ta mutu lokacin da jirgin ƙasa ya murkushe mota a Abuja […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *