Al ‘ummar yankin ƙaramar hukumar Nafaɗa a Jihar Gwambe suna fuskantar wani yanayi mai tsoro da fargaba sakamakon ɓullar wata cuta da ta laƙume rayukan yara da matasa sama da talatin.
Cutar wadda ta fara kunno kai a cikin farkon watan Fabrairun wannan shekarar da muke ciki, ta na da alamun zazzaɓi da ciwon ciki, da ciwon ƙafa da kuma amai kamar yadda bincike ya nuna.
Bayanai daga babban asibitin garin Nafaɗa ya nuna cewar an kai samfurin cutar guda ashirin kuma sakamakon guda goma sha ɗaya ya nuna cewar ba cutar Sanƙarau bane kamar yadda ake hasashe da farko.
Hakazalika bisa bayanan da suke da shi akwai mutane guda bakwai da suka rasu a wajensu, sauran mace-macen da ba sa da ƙididdigarsu sun faru ne a cikin gari.
Sakataren Gudanarwa na Babban Asibitin garin Nafaɗa, Mista Kefas K. Silanda, yayi ƙarin bayani da kuma tabbatar mana da yanayın cutar, adadin waɗanda suka mutu a asibitin da matakan da likitoci suka ɗauka na gwajin sanfurin cutar.
Daga bisani Muryar Amurka ta kai ziyara gidan wani wanda aka masa rashi sakamakon cutar, inda ya shaida mana cewa ‘yarsa ta fara rasuwa a farkon wannan watan na Maris, yanzu kuma ɗansa ya rasu.
Ya ƙara da cewa kwata-kwata ciwon idan ya kama yara baya wuce sa’o’i 48 sai mutuwa.
KU KUMA KARANTA:’Yan sa kai sun yi wa limami yankan rago a Zamfara
Ɗan Majalisar Dokoki mai wakiltar Nafaɗa ta Arewa Muhammed Tahir, Ɗan Galadiman Nafaɗa, ya ce bisa rahotan da aka ba shi, mutane sama da talatin ne suka mutu a sanadiyar cutar.
Wani mahaifiyin yara guda biyar ya ce a dole ya hana yaransa zuwa makaranta don bai san abin da zai faru ba.
Kamar yadda bayanai suka nuna cutar ta fara bayyana ne a wata makaranta a cikin garin na Nafaɗa da ke jihar Gwambe.