Wasu ‘yan damfara da suka tursasa wata mace cire kuɗi a banki sun shiga hannu

A jiya da misalin ƙarfe huɗu saura minti goma, wani ma’aikacin banki ya lura cewa wata mace da ke hulɗa da bankin ‘yar shekara 64 ta kasance cikin ruɗewa, ana ta kiran wayarta akai-akai, inda take ta hanzarin ta ciri Naira dubu ɗari shida.

Mai bada kuɗin ya tambaya menene matsalar ta, sai matar tace zata mutu idan ta faɗa masa, nan take aka tuntubi jami’an ‘yan sanda daga reshen Unguwar Ogudu a Legas.

‘Yan sanda sun kama biyu daga cikin ‘yan damfara da suka haɗarda Uche Awaize mai shekaru 45 da Osadebe Aigbe mai shekaru 35 a cikin ‘yan damfara uku da ke jiranta a wajen bankin, yayin da na ukunsu ya tsere.

Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun fara karɓar Naira dubu 90 daga hannun matar, inda suka nemi ta shiga bankin ta ciro ragowar dubu 600 da take da su a ajjiye a bankin.

Ana ci gaba da ƙoƙarin kama wancan da ya tsere.

Ga fuskokinsu koda akwai wani ko wata da suka taɓa yiwa haka a baya, don tantance su kuma su ba da shaida a kansu, kuma watakila a kwato kudaden da suka damfara a hannun wasu mutanen.


Comments

One response to “Wasu ‘yan damfara da suka tursasa wata mace cire kuɗi a banki sun shiga hannu”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Wasu ‘yan damfara da suka tursasa wata mace cire kuɗi a banki sun shiga hannu […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *