Waɗanda Suka Yi Nasara A Zaɓen Fitar Da Gwani Na Gwamnoni A PDP

0
731

Daga; RABO HALADU.

A RANAR 25 ga watan Mayun 2022 ne aka gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnonin babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya wato PDP inda aka yi gumurzu tsakanin ƴan takara da dama.

Duk da cewa an yi zabe a kusan duka Jihohin, amma akwai wuraren da aka yi maslaha kamar Jihar Sokoto.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi nasara a zaɓen fitar da gwanin sun hada da Jihar Kano, inda Mohammed Abacha ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar. An fafata ne tsakaninsa da Adamu Yunusa Ɗan Gwani da Ibrahim Al-Amin Little da Muhiyi Magaji Rimin Gado da Jafar Sani Bello da kuma Injiniya Mu’azu Magaji wato Ɗan Sarauniya.

Sai Jihar Kaduna inda Isah muhammad Ashiru ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani. Ko a 2019 ma shi ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani inda a ƙarshe ya kara da Nasiru El-Rufai na APC.

A cikin waɗanda Isa Ashiru ya kara da su a wannan karon akwai Sani Sidi da Mukhtar Ramalan Yero da Sani Abbas da Haruna Kajuru da Shehu Sani.

A Jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan jihar Sule Lamido, ya yi nasara a yayin zaɓen fitar da gwanin. Ya kara ne da Alhaji Saleh Shehu Hadejia duk da cewa kafin zaɓen rahotanni sun ce Alhaji Bashir Adamu ya janye.

Jihar Zamfara, Dauda Lawal ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar. Kafin zaben, tsohon mataimakin gwamnan jihar Barrister Mahdi Aliyu Gusau ya sanar da janyewarsa daga takarar.

Hakan ya sa aka kara tsakanin Dauda Lawal da Ibrahim Shehu Bakauye da Hafiz Usman Nahuche da Wadatau Madawaki.

Hakazalika a Jihar Sokoto, Umar Saidu ne ya zama ɗan takarar gwamnan PDP a Jihar bayan maslahar da aka samu da ƴan takarar.

Waɗanda suka janye masa sun haɗa da mataimakin gwamnan jihar Mannir Ɗan Iya da ɗan gidan tsohon gwamna jihar wato Sagir Bafarawa da Shugaban Jam’iyyar PDP a Sokoto Bello Aliyu Goronyo.

A Jihar Gombe, Jibrin Barde ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP.

Barde ya kara ne da Jamil Gwamna da Ali Gombe da Adamu Suleiman da Gimba Ya’u da Adamu Suleiman da Babayo Ardo.

A Jihar Kebbi, Janar Aminu Muhammad Bande shi ne ya yi nasara a zaben fitar da gwani na jihar inda ya kara da Dakta Buhari Bala da Garba Haruna da Samaila Sambawa.

A Jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Kashim wanda shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar shi ne ya yi nasara ba tare da hamayya ba. Sai dai ana ta raɗe-raɗin cewa yana riƙe wa gwamnan jihar Bala Mohammed tikitin takarar ne ko da gwamnan bai yi nasara a zaɓen fitar da gwamni na shugaban ƙasa ba.

A Jihar Nasarawa, David Ombugadu ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwanin da aka yi a jihar inda ya kara da General Nuhu Angbazo. Wasu rahotanni sun bayyana cewa kafin zaɓen Mista Labaran Maku ya janye daga takarar.

A Jihar Borno, Alhaji Ali Mohammed Jajari ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin bayan karawarsa da Mohammed Imam.

A Jihar Adamawa, gwamnan jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri ne ya yi nasara a yayin zaɓen fitar da gwani. Rahotanni sun ce jam’iyyar Gwamnan ya yi nasara ne ba tare da hamayya ba bayan wata kotu a Abuja ta sanar da rashin cancantar abokin takararsa Ambasada Jamil Abubakar Waziri.

A Jihar Legas, wanda jam’iyyar PDP ta sanar ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani shi ne Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor

Mista Adediran ya yi nasara ne bayan ya kara da abokin takararsa Dacova David Kolawole.

A Jihar Benue kuwa, kakakin majalisar jihar Titus Uba ne ya yi nasara a yayin zaben fitar da gwanin bayan ya kayar da mataimakin gwamna mai ci a jihar Injiniya Benson Abounu.

Kamar jihar Benue, kakakin majalisar dokokin Jihar Delta Sheriff Oborevwori ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar.

Mista Sherif ya kara ne da Olorogun David Edevbie sai kuma sanatan jihar mai wakilar kudancin jihar James Manager.

Leave a Reply