Uwa da ‘ya’yanta 5 sun mutu a Kano, sakamakon cin dambu

0
77
Uwa da 'ya'yanta 5 sun mutu a Kano, sakamakon cin dambu

Uwa da ‘ya’yanta 5 sun mutu a Kano, sakamakon cin dambu

Wata mata da ‘ya’yanta biyar sun mutu gaba ɗaya bayan da suka ci dambu, a ƙauyen Karkari da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano.

Wani maƙwabcin iyalan, Garba Muhammad ya shaida wa manema labarai cewa, saboda fatara da talauci da kuma yunwa da iyalan gidan suke fama da su, matar wadda daman mijinta ya rasu, wadda kuma ita ke kula da ‘ya’yan nata biyar ta yi amfani da dusar gero da ta daɗe a ajiye, har ma ta lalace domin dafa yi musu dambu su ci, saboda tsananin yunwa da suke fama da shi.

Garba Muhammad ya ce, lamarin ya faru ne ranar Alhamis, a gidan mijin matar marigayi Malam Abdulkarim.

KU KUMA KARANTA:Wani mutum ya gutsire mafitsara da leɓen wani yaro ya cinye (bidiyo)

Malam Garba ya ce ”cin wannan dambu ne ya yi sanadin mutuwar iyalan gidan su shida haɗi da mahaifiyar tasu”

Waɗanda suka mutun sun haɗa da, mahaifiyar mai suna Alhaƙatu Abdulkarim da ‘ya’yanta biyar -; Bashir, Firdausi,Hafsat, Usman da kuma Jamilu.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce iyalan su shida da suka ci abincin an garzaya da su babban asibitin Gwarzo, kuma a can likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Sai dai ya ce, an fara gudanar da bincike domin tabbatar da ainihin abin da ya yi sanadin mutuwar tasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here