Mutane 4 sun mutu, 21 sun samu raunuka sakamakon fashewar Bom a Yobe

0
46
Mutane 4 sun mutu, 21 sun samu raunuka sakamakon fashewar Bom a Yobe

Mutane 4 sun mutu, 21 sun samu raunuka sakamakon fashewar Bom a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mutane 4 ne suka mutu, 21 kuma sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani Bom a kan hanyar Katarko zuwa Goniri a ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe, a daren jiya juma’a. Wadanda lamarin ya rutsa da su, galibi ’yan garin Gotala ne, suna kan hanyarsu ta zuwa babbar kasuwar Buniyadi ne a lokacin da motarsu ta taka bama-baman da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka saka.

A lokacin da Neptune Prime ta ziyarci asibitin ƙwararru na Damaturu, ta ga an kai gawarwakin mutane huɗu da suka mutu sakamakon fashewar bam ɗin zuwa gida don yi musu jana’iza yayin da sauran ke karɓar kulawa a asibitin ƙwararru da kuma asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe dake Damaturu.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya kashe mutane 5 ‘yan gida ɗaya a Kano

Garin Gotala dai na can ne a bakin dajin Sambisa inda ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka shafe shekaru suna gudanar da ayyukansu na ta’addanci.

Wata majiyar kuma ta ce, wasu ‘yan banga da motocin soji suma sun taka bama-baman da aka binne a ranar Juma’a a daidai wannan hanya inda wasu suka mutu ko kuma suka jikkata.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin ba ta fitar da wata sanarwa ba.

Dangantakar waɗanda abin ya shafa da aka zanta da su a asibitoci sun yi ƙira ga gwamnatin jihar Yobe da ta gaggauta sake gina hanyar da ta lalace domin daƙile ayyukan ‘yan tada ƙayar bayan kasancewar rayuwar al’umma da kafa sojoji a Goniri na cikin haɗari.

Leave a Reply