UNICEF, WHO, CDC sun yi haɗin gwiwar samar da rigakafin ƙyandar biri

0
17
UNICEF, WHO, CDC sun yi haɗin gwiwar samar da rigakafin ƙyandar biri

UNICEF, WHO, CDC sun yi haɗin gwiwar samar da rigakafin ƙyandar biri

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya fitar da buƙatar gaggawa ta samar da rigakafin cutar ƙyandar biri ga ƙasashen da ke fama da rikici tare da haɗin gwiwar ƙawancen rigakafin Gavi, da hukumar kula da cutuka ta Afirka CDC, da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, kamar yadda ƙungiyoyin suka bayyana a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa a ranar Asabar.

Za a iya tsara yarjejeniyar samar da alluran rigakafin har miliyan 12 ya zuwa shekara mai zuwa ta 2025, gwargwadon ƙarfin kamfanonin da ke har haɗa rigakafin, a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce ƙarƙashin kwangilar, UNICEF za ta shata ƙa’idojin yarjejeniyar ta samar da rigakafin tare da kamfanonin yin alluran rigakafin.

Wannan zai baiwa UNICEF damar saya da jigilar alluran rigakafi ba tare da ɓata lokaci ba, da zarar an tabbatar da kuɗaɗen, buƙatu, tsare-tsare da kuma ƙa’idoji.

KU KUMA KARANTA:Yaran Najeriya sun cancanci samun ilimi cikin kwanciyar hankali – UNICEF

Sanarwar ta ƙara da cewa WHO na nazarin bayanan da masana’antun suka gabatar a ranar 23 ga watan Agusta, kuma tana sa ran kammala bitar bayanan domin gaggauta soma amfani da ita nan salaam alaikumda tsakiyar watan Satumba.

A farkon watan Agusta, hukumar ta WHO ta ayyana annobar kyandar biri a matsayin matakin gaggawa na kiwon lafiyar jama’a a duniya bayan barkewar cutar a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, wadda ta bazu zuwa kasashe makwabta.

An sami fiye da mutane 18,000 da ake zargin sun kamu da cutar a Kongo a wannan shekara, tare da mutuwar mutane 629, yayin da aka tabbatar da sama da mutane 150 a Burundi, in ji Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here