Ummukulsum: Kotu ta baiwa gwamnatin Kano umarnin samar wa ɗan China tafinta

1
743

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

A yau Talata ne wata babbar kotun jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta samar da mai tafinta ga wani ɗan kasar China, Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa ƴar Nijeriya, mai suna Ummukulsum Sani (Ummita), mai shekaru 22.

Wanda ake zargin na fuskantar tuhuma kan aikata laifin kisan kai, wanda ya saɓa da sashe na 221 na kundin laifuffuka.

Da a ka sake gurfanar da Quanrong Lauyan wanda a ke ƙara, Muhammad Dan’azumi, ya bukaci kotun da ta samar da mai fassarar yare (tafinta) ga wanda ya ke karewa, inda ya dogara da sashe na 36(6)(a)(b) (c) na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).

“Mai girma alkali, wanda ake tuhuma ba ɗan Najeriya ba ne. Yin amfani da Ingilishi a cikin kotu a matsayin yare na iya kasa fahimtar wanda nake kare wa shi kuma yana iya kasa fahimtar tuhumar da ake yi masa.

“Wanda ake tuhuma yana da damar samun mai tafinta daga Ingilishi zuwa yaren Sinanci, ‘yancinsa ne na Tsarin Mulki,” in ji shi.

Da ko a ka tambayi wanda ake tuhuma ko ya fahimci harshen turancin sai ya ce a’a.

Neptune prime ta rawaito lauyan masu shigar da kara na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya shaida wa kotun cewa ya umurci daraktan shigar da kara, DPP da ya rubuta wasika zuwa ofishin jakadancin kasar Sin da al’ummar kasar Sin da ke Kano inda ya bukaci a samo mai fassara a madadin wanda ake tuhuma.

“Wanda ake tuhumar ya yi magana da Turanci mai kyau a ranar da aka ɗage sauraron karar, a ranar 29 ga Satumba.

“Idan muka samu mai fassara za mu gama shari’ar cikin kankanin lokaci,” in ji Mista Abdullahi Lawan.

Mai shari’a Sanusi Ado-Ma’aji ya umurci gwamnatin jihar Kano da ta rubutawa ofishin jakadancin kasar Sin domin samar da tafinta ga wanda ake kara.

Ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali sannan ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 27 ga Oktoba domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Ana tuhumar Quanrong ne da daɓa wa Ummukulsum wuka har lahira a unguwar Kabuga da ke cikin birnin Kano bisa wasu dalilai da ba a tabbatar da su ba.

An fara gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun Majistare bisa irin wannan tuhuma. Sai dai lauyan gwamnati ya nuna rashin amincewarsa na ci gaba da gurfanar da shi gaban kotun, inda ya nanata cewa karamar kotun ba ta da hurumin sauraron irin wannan karar.

1 COMMENT

Leave a Reply