Turji ya sha da ƙyar tare da munanan raunuka a harin da sojoji suka kai masa

1
790

Rahotanni da dama daga jihar Zamfara na nuni da cewa gawar shahararren ta’addan nan Bello Turji, bata cikin ‘yan ta’adda 37 da rundunar sojojin saman Najeriya ta kama a ranar Asabar 17 ga Satumba, 2022.

Jaridar Daily Reality ta tuna cewa jami’an soji sun kai harin bam a maɓoyar ‘yan bindigar. Duk da cewa Turji ya tsere, an ruwaito cewa ya samu munanan raunuka yayin da aka kashe mabiyansa 37.

Turji shararren sarkin yaƙin ‘yan fashi ne wanda ke iko da wata babbar ƙungiya. Ya kasance yana jagorantar hare-hare a Zamfara da wasu sassan arewa maso yammacin ƙasar.

Zamfara dai na ɗaya daga cikin wuraren da ake fama da matsalar ‘yan ta’adda da garkuwa da mutane. Wannan lamari ya jefa da yawa daga cikin mazauna jihar cikin ƙunci tare da shafar harkokin kasuwanci da sauran ayyuka da dama a jihar.

Gwamna Bello Matawalle na jihar ya buƙaci mazauna jihar da su ɗauki makamai su kare kansu a kokarinsa na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da hare-hare a jihar.

An kuma ruwaito cewa Gwamnan ya tara jami’an tsaron al’umma, waɗanda ya ba su ƙarfin bindigogi sama da 7000. Sai dai ana ci gaba da kai hare-hare.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here