Daga Fatima MONJA, Abuja
Wata tsohowa, Doreen Breen mai shekaru 93 tayi gamo da alajalin ta yayin da ta fita haraban gida domin zubda shara.
Tsohuwar, ta mutu ne bayan ɗiyar ta Hezal Smith ta haye kanta da mota kirar Audi A3 yayin da take yin kwana don fita yawo.
Mrs Smith ta kasance da diyarta a gida ɗaya inda a watan mayu ta gamu da alajalin ta. Da ake tambayan yarinyar marigayar, ta dage akan ba gaganci ne yasa tayi ba kafin tayi kwana sai da ta duba madubi amma bata hango tsohuwar mahaifiyyar ta ba.
Batayi aune ba kuma ta take burki, yayin da taji tayi arangama da wani abu lokacin tana yunkuri fita zuwa Eckington, Derbyshire dake kasar Ingila.
Mrs Breen ta kasance cikin hayyacin ta kuma tana magana bayan afkuwan lamarin, kuma ankai ta asibitin Chestfield, amma bayan kwanaki biyu ta mutu sakamakon raunuka da bugun kwakwalwa kamar yadda kotun Chestfield Coroner ta bayyana.
Yan sandan Derbyshire sun binciki mutuwar amma ba cikakken shaidan aikata laifin ganganci.
Mataimakiyar Coroner miss Susan Evans ta yanke hukuncin cewa Ms Breen ta mutu sakamakon wani hatsarin motar ‘yar ta bayan bugeta cikin rashin sani, wanda ya haifar mata da bugun kwakwalwa da wasu raunuka.