Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasu
Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasuya rasu a ranar Alhamis kwana ɗaya da cikarsa shekaru 78 a duniya, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Dan Kamarun ya kasance shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) na tsawon shekaru 29 daga 1988 har zuwa lokacin da aka hambarar da shi a wani lamari mai ban mamaki a shekarar 2017.
Ya kuma riƙe muƙamin shugaban hukuma ta FIFA na riƙo daga 2015-2016 bayan da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta dakatar da Sepp Blatter.
Hayatou, wanda ɗan’uwansa ne firaministan kasar Kamaru, ya kasance mai kula da harkokin wasanni a tsawon rayuwarsa.
Ya kasance mamba na kwamitin Olympics na kasa da kasa daga 2001-2016, bayan haka ya zama mamba na girmamawa.
A shekarar 2011 hukumar ta IOC ta ladabtar da Hayatou kan rawar da ya taka a baɗakalar karɓar cin hanci a hukumar ta FIFA.
KU KUMA KARANTA;An dakatar da Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda ya fusata ‘yan kallo
An tsawatar masa bayan da shirin BBC Panorama ya yi iƙirarin cewa ya ƙarbi kusan dala 20,000 daga rusasshen kamfanin tallan wasanni na ISL a shekarar 1995.
Hayatou ya musanta cin hanci da rashawa kuma ya ce kuɗaɗen kyauta ne ga ƙungiyarsa.
Zamansa na shugabancin kwallon kafar Afirka ya sa wasan ya samu ci gaba duk da cewa ana zargin Hayatou da jan kafa wajen kawo sabbin sauye-sauye.
Hayatou ya ƙalubalanci Blatter a matsayin shugaban FIFA a shekarar 2002, amma ya sha kaye yayin da ƙasashen Afirka da dama suka yi watsi da shi a ƙuri’ar adawa da Swiss.