Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya amsa gayyatar EFCC
A yau laraba aka ce tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa EFCC ta yi masa.
A wata sanarwa da Daraktan ofishin yaɗa labarai na Yahaya Bello, Ohiare Michael ya fitar a ranar Laraba, an tabbatar da cewa Bello ya yanke shawarar karrama wannan gayyata ne biyo bayan tattaunawa da ya yi da iyalansa, da ƙungiyar lauyoyi, da kuma abokan siyasa.
“Muna fatan hukumar za ta gudanar da aiki bisa ƙwarewa da kuma mutunta ‘yancinsa a matsayin ɗan ƙasa,” in ji sanarwar.
Tsohon gwamnan, wanda a baya an ayyana nemansa bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da sauran ayyukan almundahana da suka kai Naira biliyan 80.2.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci Yahaya Bello da ya miƙa kansa
Ya kuma samu rakiyar manyan ‘yan Najeriya zuwa ofishin hukumar.