Tsawa da walƙiya sun yi ajalin shanu 8 jihar Ondo
Daga Shafa’atu Dauda, Kano
Aƙalla Shanu takwas ne suka mutu a sakamakon wata Tsawa da Walƙiya a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, Olayinka Ayanlade, ne ya tabbatar wa da kafar talabijin ta Channels faruwar lamarin a garin Ori-Ohin na ƙaramar hukumar Ose, ranar Lahadi da yamma a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
KU KUMA KARANTA:Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 5 a Yobe
Olayinka ya ƙara da cewa, tuni rundunar ta fara ɗaukar mataki saboda kada lamarin ya haifar da fitina a jihar.
A shekarar 2019 mah irin wannan lamari ya taɓa kashe shanu 36, lokacin da aradu ta auka wa yankin Ifedore na jihar ta Ondo.









