Rundunar Sojan Najeriya ta ba da lambobin waya na musamman da ‘yan ƙasar za su iya kira don ba da rahoto kan matsalar tsaro, yayin da wasu ƙasashe ke bayyana fargabar harin ta’addanci a Abuja.
Duk da cewa ba yanzu rundunar ta fara fito da lambobin kiran ba, ta ɗauki matakin na yanzu ne yayin da wasu ƙasashen waje ke shawartar ‘yan ƙasashen nasu da su fice daga Abuja, na waje kuma kar su shiga.
Ƙasashen Amurka da Birtaniya da Kanada da Jamus da Ireland da Bulgaria da Denmark ne suka nuna fargabar zuwa yanzu.
Rundunar ta wallafa lambobin a shafukanta na zumunta a ranar Juma’a, inda ta nemi ‘yan ƙasa su ba da rahoton da zai taimaka mata wajen daƙile barazanar tsaro.
“Ku taimka wa Rundunar Sojan Najeriya da duk wani bayani da zai taimaka wajen daƙile matsalar tsaro ta hanyar kira ko saƙon tes ko kuma ta WhatsApp ta waɗannan lambobi,” a cewar sanarwar.
Lambobin su ne:
- 193
- 07017222225
- 09060005290
- 08077444303
[…] Source link […]