Tinubu zai sake fasalin Fannin mai da iskar gas

0
126

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tattaɓa hannu kan dokar sake fasalin man fetur da iskar gas domin ya sanya Najeriya a matsayin ƙasar da aka fi son zuba jari a ɓangaren mai da iskar gas a Afirka.

A cewar wata sanarwa da mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce an tsara da kuma sauya manufofin ne tare da hadin gwiwar manyan ma’aikatu da hukumomi kamar ma’aikatar shari’a ta tarayya, ma’aikatar kuɗi ta tarayya ma’aikatar man fetur ta tarayya, ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta tattalin arziƙi ta tarayya, ma’aikatar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa, da kuma hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa ta Najeriya.

An yi gyare-gyaren ne domin ƙara haɓaka tattalin arziƙin Najeriya da kuma ƙara ƙarfinta a kasuwar mai da iskar gas ta duniya.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya naɗa ɗan Ganduje darakta a hukumar lantarki ta REA

Ya ce ma’aikatar yaɗa labarai ta tarayya da wayar da kan jama’a ta ƙasa za ta sanar da cikakkun bayanan a hukumance, wanda zai nuna wani gagarumin mataki na samun ci gaba mai inganci a ɓangaren mai da iskar gas a Najeriya.

Ya ce mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin makamashi zai ci gaba da haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki da aka ambata kan yadda ake aiwatar da waɗannan umarni, tare da jaddada ƙudirin gwamnatin na samar da ci gaba mai ɗorewa da ci gaba a masana’antar makamashi.

Leave a Reply