Tashar ruwa ta Lekki: Gwamnatin Buhari ce ta fara aiki ta kuma kammala shi- Bashir Jamoh

A ranar Litinin ne shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin gina katafariyar tashar jiragen ruwa da ke Lekki aikin da aka yi akan dala biliyan 1.5 a yankin Ibeju-Lekki, a jihar Legas.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya shaida cewa aikin katafariyar tashar jiragen ruwan na haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnatin tarayya, jihar Legas da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

“Kuma muna farin ciki da cewa wannan yana faruwa a lokacin gwamnatin shugaba Buhari, An fara a lokacin mulkinka, kuma an kammala shi a lokacinku.

“Lallai mun yi farin ciki cewa jiragen da za su shigo nan za su ninka girman jiragen da ke shigowa a tashoshin TinCan da Apapa har sau hudu.

“Don haka babban aiki ne na more rayuwa, kuma haƙiƙa muna farin ciki cewa a lokacinku, wani sabon abu ya shigo ƙasar kuma zai samar da dubunnan ayyukan yi kai tsaye da kuma ayukkan yi ga ɗaukacin jama’a.

Wannan aiki ɗaya ne daga cikin ayyukan da muke jin dadin kammaluwarsa tare da dukkan abokan hulɗa da hukumomin da suka yi namijin ƙoƙari wajen ganin mun kawo abin da muke gani a nan a yau,kuma tabbas muna godiya ga ‘yan ƙasar da suka fahimci cewa wannan jari ne ya zo musu.” inji gwamnan Legas.

Tun da farko, Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya, Mohammad Bello-Koko, ya ce tuni wasu ƙasashe makwabta suka fara nuna sha’awarsu ta fara kawo hajarsu ta tashar ruwa mai zurfi ta Lekki. “Mafarki ne ya zama gaskiya, zai taimaka wajen kawo ƙarin kaya, da ƙarin ayyukan yi, zai zama abin koyi ga sauran manyan tashoshin jiragen ruwa a Najeriya.

“Tuni dai hukumar ta NPA ta fara samun kayan aiki da za su sauƙaƙa fitar da kaya cikin sauƙi da kuma sukuni, wasu ƙasashen makwabta sun fara nuna sha’awar shigo da kayansu ta tashar jiragen ruwa na Lekki,” in ji shugaban NPA.

Shima da yake nasa jawabin, babban daraktan hukumar kula da harkokin jiragen ruwa Najeriya, Dr. Bashir Yusuf Jamoh, ya ce, “Ina ɗaya daga cikin masu farin ciki a nan, domin a yau muna ganin bayyanar ɗaya daga cikin mafi kyawun tashar jiragen ruwa, ba kawai a Najeriya ba har ma a Afirka gaba ɗaya.

“Masana’antar ruwa na daya daga cikin manyan bangarorin, bayan manafetur da iskar gas don ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

“A yau muna ganin nasarar ɗaya daga cikin mafi kyawun tashar jiragen ruwa a yammacin Afirka da ake sa ran za ta zuba kasa da dala biliyan 360 da kuma samar da aikin yi ga ‘yan Najeriya da ba su gaza 190,000 ba”.

“Kun san lokaci zuwa lokaci muna fuskantar ayyukan da aka yi watsi da su, wannan shi ne karo na farko da muke ganin sadaukarwar siyasa kan aiwatar da ayyukan gwamnati.

“Idan aka ƙirga shekarun da aka fara aikin zuwa yanzu, zai dace a ce wannan gwamnati ce ta fara aikin kuma ta kammala shi saboda jajircewa da mayar da hankali kan ma’aikatarmu.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *