Taron bunƙasa cinakayya tsakanin Damagaram, Daura, Jigawa da Kano

0
52
Taron bunƙasa cinakayya tsakanin Damagaram, Daura, Jigawa da Kano

Taron bunƙasa cinakayya tsakanin Damagaram, Daura, Jigawa da Kano

A ci gaba da sake bunƙasa hulɗar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar, tun bayan warware rigimar da ta biyo bayan takunkuman ECOWAS, ƙungiyar PRODAF ta inganta tsarin kasuwanci tsakain Damagaram, Daura, Jigawa da Kano, ta yi wani babban taro a Damagaram, Janhuriyar Nijar, da zummar komawa kan shirin nan na bunkasa nau’ukan noma da kasuwancin da kowannensu ya fi yin fice a kai.

Muhammad Rufa’i, Babban Jami’in saukaka kasuwanci tsakanin Nijar da Najeriya, ya yi karin bayani ma wakiliyar Sashin Hausa a Damagaram, Tamar Abari da cewa daga abin da aka cimma a wurin taron na Damagaram za a dora.

KU KUMA KARANTA:Mun tafka mummunar asara – ’Yan kasuwa

‘Yan kasuwan kasashen biyu, musamman ma daga garuruwan nan hudu da su ka fai cinakayya da juna, kan koka kan tsaurin ka’odojin cinakayyar, wadanda kan gurgunta harkokin tattalin arzikinsu alhalin kuwa za su amfani juna, ganin kowannensu na da wadatar wani abu da sauran ke matukar bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here