Tag: Kuɗi
-
Ɗan Afirka ta Kudu ya maye gurbin Ɗangote a matsayin wanda ya fi kuɗi a Afirka
Ɗan Afirka ta Kudu, Johann Rupert, ya sha gaban attajirin Najeriya, Aliko Ɗangote, a matsayin wanda ya fi kuɗi a nahiyar Afirka. Sabon jadawalin attajiran da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta fitar ya nuna cewa Ɗangote ya sauko daga matsayin ne bayan dala biliyan $3.8bn sun ragu daga cikin arzikinsa. Mujallar…
-
DSS ta ce shugabanta bai sace kuɗin tallafi na ma’aikatan hukumar ba
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya DSS ta musanta zarge-zargen da ake yi kan cewa babban daraktan hukumar Magaji Yusuf Bichi ya yi sama da faɗi da kuɗin tallafi na ma’aikatan hukumar. Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ne ya fitar da sanarwar inda ya musanta zargin da wani Jackson Ude ya yi…
-
Ma’aikatun da suka fi samun kuɗi a kasafin 2024
A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da sauran ɓangarori a kasafin shekarar 2024 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar. A ranar Laraba Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 27.5, ba tare da bayanin kason da ware wa ma’aikatu da ɓangarori ba, lamarin da…
-
Babu ranar daina amfani da tsofaffin kuɗi — CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira kuma za su ci gaba da kasancewa halastattu har bayan wa’adin 31 ga watan Disamban 2023 da aka sanya. Wata sanarwa da daraktan sadarwa na CBN, Isa AbdulMumin ya fitar, ta buƙaci ’yan Najeriya su ci gaba da amfani da…
-
An bayyana kuɗin da maniyyata aikin hajjin 2024 za su ajiye a Kano
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano ta ƙaddamar da shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024 a hukumance. Alfijir Labarai ta rawaito Darakta Janar na hukumar Alhaji Laminu Rabi’u ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai, wanda ke alamta fara shirye-shiryen aikin na bana a gudanar a ofishinsa . Laminu ya ce hukumar alhazai…
-
Wani ɗan Sakkwato ya damfari mutane 12 kuɗi har naira miliyan 325
Kotu ta yankewa wani ɗan Sakkwato, Ahmad Abubakar Ahmad hukuncin ɗaurin shekaru 87 a gidan yari, bisa samunsa da laifin damfarar mutane 12 kuɗaɗe daban-daban da sunan sa hannun jari a ofishinsa na canji. A cewar EFCC Ahmad ya kuma yi wa waɗanda abin ya shafa alƙawarin ba su jari daga kashi 50% zuwa 100% na jarin su duk…
-
Akwai yiwuwar masu amfani da shafin X su fara biyan kuɗi
Mai kamfanin sada zumunta na dandalin X wanda a baya ake ƙira da Twitter, Elon Musk, ya ce masu amfani da shafin ka iya fara biyan kuɗi domin amfani da shi. Attajirin mai kuɗin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci wani zauren tattaunawa da firaministan Isra’ila, Benyamin Netanyahu a jihar California. Wakiliyar…
-
Gwamna Yobe ya ba da tallafin kuɗi a mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa
Daga Ibraheem El-Tafseer Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya ƙaddamar da tallafin kuɗi Naira dubu ɗari (N100,000) kowane ga kimanin mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin jihar a ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na ‘COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus’ (NG-CARES). Wannan shiri na NG-CARES shiri ne wanda ake aiwatar da…
-
Raba wa talakawa kuɗi don rage raɗaɗin cire tallafin mai ba shi ne mafita ba – Gwamnan Kaduna
Daga Ibraheem El-Tafseer Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya soki tsarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi na raba wa ‘yan Najeriya tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai. Ita dai gwamnatin ta ce za ta raba wa ‘yan ƙasar miliyan goma sha biyu ne, daga cikin su sama da miliyan…
-
‘Yan bindiga sun yi barazanar auran matan da aka sace a Zamfara, sun buƙaci a ba su naira miliyan 12 (Bidiyo)
Wasu mata huɗu da aka yi garkuwa da su da suka haɗa da ɗalibar kwalejin fasaha da kimiyya ta jihar Zamfara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, sun tayar da ƙura kan barazanar da masu garkuwar ke yi na auran su idan iyayensu suka ka sa biyan kuɗin fansa naira miliyan 12. Waɗanda…