Tag: Ɗan fashi
-
‘Yan sanda sun cafke wani ɗan fashi da ake nema ruwa a jallo
A ranar 17 ga watan Oktoba 2023, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta yi nasarar cafke wani ɗan fashi da aka daɗe ana nema ɗan kimanin shekara 30 mai suna Shu’aibu Abubakar. Shua’aibu dai ya kasance cikin jerin waɗanda rundunar take nema ruwa a jallo tun da daɗewa. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, shi ne ya bayyana hakan a shafin su na X a ranar Laraba. Sanarwar ta fito…
-
Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) reshen jihar Kebbi, a ranar Lahadin da ta gabata ta tabbatar da kisan wani ma’aikacinta mai suna Aminu Abdullahi da wani da ake zargin mai safarar motoci ya yi a ƙaramar hukumar Yauri ta jihar. Kakakin hukumar, ASC Mubarak Mustapha, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya…
-
‘Yan sanda sun kashe wani ɗan fashi a babbar hanyar a Gombe
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta ce jami’anta sun kashe wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne a wata arangama da suka yi, inda suka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 daga hannun ɗan fashin. Mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Sharif Sa’ad ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake…
-
Rundunar sojin sama taci galaba kan Halilu Tubali, ƙasurgumin dan fashin daji a Zamfara
Hukumomi a Najeriya sun ce sun tarwatsa sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ya addabi sassan jihohin Zamfara da Katsina, tare da gomman yaransa. Rundunar sojin saman ƙasar ta tabbatar wa BBC cewa an kashe Halilu Tubali da yaransa a wani hari da jirgin yaƙi da dakarunta suka kai a ƙarshen makon jiya. Majiyoyi…
-
‘Yan sanda sun kama tsohon soja da ya zama ƙasurgumin dan fashi a Zamfara
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani ƙasurgumin ɗan fashin daji a kan hanyarsa ta shiga jihar. An kama ɗan fashin mai suna Sa’idu Lawal da bidigar AK-47 guda ɗaya da AK-49 ɗaya da harsasai masu tarin yawa. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan…