Sojoji sun yi nasarar sako rukunin ƙarshe na fasinjojin jirgin ƙasan da aka yi garkuwa da su

1
672

Kwamitin shugaban ƙasa mai mutane bakwai da babban hafsan sojin ƙasa (CDS), Janar Lucky Irabor ya tara, ya samu nasarar sako rukunin ƙarshe – sauran fasinjoji 23 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su bayan harin da aka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Neptune Prime ta fitar wacce Farfesa Usman Yusuf, sakataren babban jami’in tsaro na ƙasa (CDSAC) ya fitar.

An yi sakin fasinjojin ne a ranar Laraba, 4 ga Oktoba, 2022 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma. “Ina mai farin cikin sanar da al’umma da duniya baki ɗaya cewa da karfe 1600Hrs (4:00pm) yau Laraba 5-10-2022, kwamitin mutum bakwai na shugaban ƙasa wanda babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor ya tara. An sako sauran fasinjoji 23 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su bayan harin da aka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a ranar 28-3-2022″, cewar Farfesa Yusuf.

“Al’ummar ƙasa na bin bashin godiya ga Sojojin Najeriya ƙarƙashin jagorancin CDS wadanda suka shirya da jagorantar aikin tun daga farko har ƙarshe. Dukkan Hukumomin Tsaro da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya sun ba da gudunmawa sosai ga wannan aiki.

“Tallafin da Shugaban ƙasa kuma Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari GCFR ke bayarwa shi ne ya sanya hakan ya yiwu. “Mambobin wannan kwamiti suna godiya da irin karramawa da alfarmar da aka ba su na kasancewa cikin wannan aikin agaji.

Ya ƙara da cewa “Allah Madaukakin Sarki Ya Warkar da Raunukan Mu, Ya kuma kawo mana zaman lafiya a ƙasarmu.”

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here