Connect with us

Ƙasashen Waje

Shugaban Senegal ya naɗa ubangidansa, Sonko, a matsayin firaiminista

Published

on

Sabon shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya naɗa uban-gidansa kuma fitaccen ɗan siyasar nan da ya goyi bayansa Ousmane Sonko a matsayin firaiminista.

Sonko, wanda babban ɗan hamayya ne ga tsohon shugaban ƙasar Macky Sall, yana da matuƙar farin-jini a tsakanin matasan ƙasar, ko da yake an haramta masa tsayawa takara a zaɓen ranar 24 ga wata Maris sakamakon zargin ɓata suna. Sai dai ya musanta wannan zargi.

“An naɗa Ousmane Sonko a matsayin firaminista,” a cewar Oumar Samba Ba, babban sakatare a fadar shugaban ƙasa, a yayin da yake jawabi a gidan talbijin na ƙasar wato RTS.

Sonko, mai shekara 49, ya kwashe shekaru biyu yana kai ruwa rana da tsohuwar gwamnatin kasar, lamarin da ya kai ga yin jerin zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.

KU KUMA KARANTA: Macky Sall ya taya ɗan takarar jam’iyyar hamayya na Senegal murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa

Daga bisani an haramta masa tsayawa takara amma ya buƙaci magoya bayansa su goyi bayan Faye a zaɓen shugaban ƙasar.

Mutanen biyu sun yi yaƙin neman zaɓe mai taken “Diomaye is Sonko,” wato Sonko ‘Diomaye da Sonko ɗaya suke’ inda Sonko ya riƙa kira ga magoya bayansa su zaɓi Faye, wanda ya lashe zaɓen da fiye da kashi 54 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Faye ya sha rantsuwar kama aiki ranar Talata inda ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye a ƙasar.

Da yake magana bayan naɗa shi a matsayin firaiminista, Sonko ya ce zai miƙa wa shugaban ƙasa Faye jerin sunayen mutanen da za a bai wa muƙaman ministoci domin ya amince da su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Published

on

Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Published

on

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.

Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.

COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.

Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.

Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Published

on

An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Daga Ibraheem El-Tafseer

Me magana da yawun Shelkwatar zaɓe ta Iran Dakta Muhsin Elsami, ya sanar da cewa, an kammala lissafi ƙuri’a Miliyan 25 na zaɓen shugaban ƙasar Iran wanda aka fara ranar juma’a.

‘Yan takara 6 ne suka tsallake matakin ƙarshe yayin da 2 suka fice saboda ra’ayin kai, ana zaɓe saura kwana 2.

Dakta Mas’ud Pezeshkian shi ne kan gaba da ƙuri’a Miliyan 10.415.991

Dakta Sa’ed Jalili ya samu ƙuri’u Miliyan 9.473298

Se kuma Dakta Qalibaf ya samu ƙuri’a Miliyan 3.383.340

Sai Ayatullah Musfata ya samu ƙuri’a 206.397.

Yanzu haka an fitar da Dakta Baqir Qalibaf da Ayatullah Musfata da suke da ƙarancin ƙuri’a, ya rage saura Dakta Jalili da Dakta Mas’ud Pezeshkian da ken gaba.

KU KUMA KARANTA: Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama

Jami’i Muhsin Elsami ya sanar da cewa za’a shiga matakin zaɓe na 2 ranar Juma’a mai zuwa inda za a kara tsakanin Dakta Jalili da Dakta Mas’ud.

Cikin su duk wanda ya samu kaso 50 ya zama shugaban ƙasar Iran, wanda zai maye gurbin Shahid Ebrahim Ra’isi wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin Helikofta, a watan da ya gabata.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like