Shugaba Tinubu ya taya kiristoci murnar bikin Ista

0
153

Domin murnar zagayowar ranar Ista, Tinubu a cikin sanarwar daya fitar a ranar juma’a, ya buƙaci kiristoci su rungumi halayen ƙauna da sadaukarwa da tausayin juna da ake dangantawa da wannan lokaci.

Sanarwar ta ruwaito me magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale yana cewar, Shugaba Tinubu ya yi jinjina ga Kiristocin Najeriya dana duniya baki ɗaya a wannan lokaci, inda ya jaddada mahimmancin ƙauna, sadaukarwa da tausayin juna a matsayin ladubban da lokacin ke koyarwa.

“Shugaba Tinubu ya ƙara da cewar, sadaukarwa da Yesu Almasihu ya yiwa jinsin ɗan adam wani darasi ne abun koyi ga shugabanni da ilahirin ‘yan Najeriya dake horo akan sadaukarwa da tausayi da juriya a fafutukar samar da dunƙulalliyar ƙasa me cike da zaman lafiya da yalwar arziƙi.”

Tun bayan ɗarewarsa kan karagar mulki a watan mayun bara, gwamnatinsa ta ɓullo da manufofi da dama da suka yi kyakkyawan tasiri akan al’umma da tattalin arziƙin Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Malamai su daina tsine wa Najeriya, su ke yi mata addu’a — Tinubu

A cewar hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS), a bara, Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur da sanyawa harkar musayar kuɗaɗe linzami, al’amarin da ya sabbaba ninkawar farashin man fetur ɗin har sau 3 da kuma ta’azzarar tsadar rayuwa a yayin da darajar naira ta yi mummunar karyewa idan aka kwatanta ta da dalar amurka, sannan hauhawar farashin kayan masarufi ta kai kaso 31.70 cikin 100.

Sai dai gwamnatin Najeriya mai cin ta sha nanata buƙatar ‘yan Najeriya su ƙara juriya game da sauye-sauyen da take kawowa, waɗanda Tinubu ya bayyana cewar za su jawo masu zuba jari zuwa ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar Afrika.

A cikin saƙonsa na bikin Ista, Shugaba Tinubu ya jinjinawa juriya da sadaukarwa ‘yan Najeriya, inda yace suna da muhimmanci wajen sake farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.

Ista biki ne da ake gudanarwa domin murnar zagayowar ranar da Yesu Kiristi ya tashi daga matattu.

Kuma wata alama ce dake nuni da samun galabar yesun akan zunubi da mutuwa.

Leave a Reply