Shugaba Buhari ya gana da fasinjojin jirgin ƙasan da aka sako

1
680

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka sako.

Ya gana da mutanen ne a Kaduna ranar Alhamis, kwana guda bayan sako sauran fasinjoji 23 da ke hannun ‘yan kungiyar Boko Haram da suka sace su.

Wasu hotuna da fadar shugaban Najeriya ta wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna Shugaba Buhari da gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar LEO Irabor da wasu jami’an gwamnati da na rundunar soja suna ganawa da fasinjojin jirgin ƙasan.

Shugaba Buhari ya gana da mutanen ne a asibitin NDA da ke Kaduna.

A watan Maris din da ya gabata ne maharan suka far wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna mai suna AK-9 inda suka dasa nakiyoyi a titin jirgin sannan suka sace fasinjojin cikinsa.

‘Yan Najeriya sun yi kakkausan suka ga shugaban kasar bisa abin da suka kira rashin yin katabus wajen ceto mutanen, inda iyalansu suka rika bin wasu hanyoyi wajen ganin an saki ‘yan uwansu.

1 COMMENT

Leave a Reply