Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
A CI gaba da kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban a Arewacin Najeriya, wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky, shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) na kasa, ya raba buhuhunan kayan abinci sama da 50 ga Zawarawa Kiristoci, Marayu da sauran al’umma mabukata daban-daban a kudancin kaduna domin tallafa musu da abincin da za su ci da kuma karfafa musu gwiwa wajen gudanar da addu’o’in ci gaba da addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaro da ke kalubalantar zaman lafiya a kasar nan.
Wannan a cewarsa, wani bangare ne na rabon Kayan abinci na shekara-shekara ga Miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fuskantar tsadar kayan abinci a kasar.
A cikin sakonsa, ya ce wannan wani bangare na kyautar watan Ramadan da yake yi ne a duk shekara ga musulmi da kiristoci domin a yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.
Rabon Kayan abincin da aka fara tun karshen makon da ya gabata ga al’ummar Musulmi da dama, a yanzu an mika shi ga al’ummar Kiristocin da ke kudancin Jihohin kasar da nufin taimaka wa mabukata kan wani mawuyacin hali.
Acewarsa, za a kara ci gaba da raba wasu kayan abinci dayawa ga al’ummar musulmi da kiristoci a wannan wata na Ramadan.
Da yake karbar kayan abincin a gidansa, Fasto Yohanna Buru, babban mai kula da Cocin Christ evangelical and life intervention Ministry, ya bayyana jin dadinsa tare da godewa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky bisa karimcin da ya nuna na tunawa da kiristocin talakawa a cikin wannan yanayin tsadar kayan abinci a kasuwanni.
Buru, ya kara da cewa yawancin Kiristoci na gab da kammala Azuminsu na kwanaki 40 da suke yi wanda za su yi amfani da shi wajen bukin ester.
A cewarsa wannan ba shi ne karon farko da Sheikh din ke aika kayan abinci ga Kiristoci da dama a yankin kudancin kasar da nufin karfafa zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi a yankin ba.
A yayin da yake jaddada cewa hakan zai inganta zaman lafiya da hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya.
Buru ya ce, za a kuma mikawa ‘yan Jaridar Kaduna tallafin kayan abinci na watan Ramadan da nufin karfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.