Shawarwari 15 da ƴan sanda suka bayar don kare kai a Najeriya

0
509

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin ɗaukar matakan tsaro domin kare makarantu da asibitoci da ma’aikatan lafiya da muhimman kayayyakin jin daɗin jama’a a fadin ƙasar.

Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi 14 ga watan nan na Agusta, 2022, kan yanayin tsaron kasar baki daya.

Shugaban ‘yan-sandan ya kuma umarci jami’an da su riƙa gudanar da sintiri da bincike akai-akai domin rage yawan aikata miyagun laifuka a Najeriya.

A kan hakan ne hukumar ‘yan sanda ta roki al’ummar kasar da su yi haƙuri da yadda za su riƙa ganin jami’ansu a wurare daban-daban da dama suna kuma tsayar da su domin gudanar da bincike.

Dangane da hakan hukumar ‘yan-sandan ta Najeriya ta fitar da wasu shawarwari ko matakai 15 da jama’a za su iya bi dpomin kare kai daga matsalolin tsaro.

Matakan kariya

Shawara ta 1. Kada ka mana takarda ko wata alama da za ta nuna aikinka ko wurin da kake aiki, musamman idan aikin naka babba ne.

Shawara ta 2. Kada ka sa hoton ɗanka ko ‘ya’yanka sanye da kayan makaranta ko bajon makarantarsu a shafukan intanet. Ku kare ‘ya’yanku.

Shawara ta 3. Idan ka je wajen wani taron biki kada ka riƙa liƙin kudi, maimakon haka ka sa kudin a wata takarda ko ambulan ka ba makaɗan.

Shawara ta 4. Kada ka je na’urar cirar kudi ta ATM ka ɗauki kuɗi masu yawan gaske ko ma ka nemi ƙarar da kuɗin da ke ciki. Ba sai ka sa Naira dubu 50 ba a ‘yar karamar jakar za ka nuna kai mai kuɗi ne.

Shawara ta 5. A kodayaushe ka goge saƙon da banki ke turo maka ta waya na hada-hadarka ta banki. Za ka iya haddace bayanin yawan kudin da suka rage maka a asusunka ba sai ka bari a wayarka ba. Ka yaga rasitinka na POS ko ATM ka jefar.

Shawara ta 6. Kada ka bi wajen da yake da duhu ko ba mutane sosai a lokacin da kake motsa jiki. Idan har za ka yi haka to ya kasance kana tare da wani da ka yarda da shi.

Shawara ta 7. Kodayaushe ka tabbatar da ka rufe ƙofar ka ko da za ka fita ne kawai ka kashe jannaretonka.

Shawara ta 8.  Kada ka taɓa sanyawa ko barin katinka na wurin aiki rataye a wuyanka idan ka fita daga wurin aiki. Ba wanda ke buƙatar sanin inda kake aiki.

Shawara ta 9. ka riƙa sanar da iyayenka ko iyalinka duk inda kake a kodayaushe.

Shawara ta 10. Kada ka aiki yaro shi kaɗai waje. Ka tabbatar ka haɗa shi da wani babba.

Shawara ta 11.  Kada ka riƙa nuna kanka cewa kai babban mutum ne ko mai kuɗi ne a unguwarku. Kana rabon manyan kudi ko wasu abubuwa.

Shawara ta 12. Ka riƙa yi a cikin sirri ya fi.

Shawara ta 13. Kada ka riƙa daɗewa bayan an tashi daga aiki a ofis ko wurin aiki har ka yi dare. Za ka iya barin aikin da ya rage maka nan gaba ko ma a gida.

Shawara ta 14. Har kullum ka riƙa kawo matakan kariya ko yadda za ka kauce wa wata matsala a duk abin da za ka yi ko inda za ka je.

Shawara ta 15. Ka san irin abubuwan da za ka sanya game da kanka a shafukan intanet.

Leave a Reply