Sarki Charles III na Ingila, yana fama da cutar kansa

0
127

Daga Maryam Umar Abdullahi

A ranar Litinin da ta gabata ne masarautar Buckingham ta bayyana cewa, Sarki Charles na 3 ya kamu da cutar sankara kuma tuni ya fara karɓar magani, duk da dai masarautar ba ta bayyana ko wacce irin sankara sabon Sarkin Ingilan ya kamu da ita ba.

Ƙasa da watanni 18 da hawa gadon sarautar, Sarki Charles mai shekaru 75 a duniya zai dakatar da ayyukan masarautar na ɗan lokaci, amma zai ci gaba da gabatar da ayyukan da suka shafi ƙasa, kuma ba zai dakatar da ayyukan da tsarin mulki ya ɗora ma shi ba, a cewar wata sanarwa da masarautar ta Buckingham ta fitar.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun sace mahalarta ɗaurin aure 35 a Najeriya

Batun cutar kansar ya bayyana ne bayan da Sarki Charles ya shafe kwanaki 3 a asibiti a watan jiya, sakamakon wata ‘yar ƙaramar tiyata da aka yi ma shi.

Masarautar ta ƙara da cewa, tun a lokacin kwanciyar ta shi a asibitin ne aka lura da wata matsalar a kwance, amma dai ba a bayar da wani ƙarin bayani ba, illa dai cewa, gwaji ya nuna Sarkin na da wani nau’in cutar kansa a tare da shi.

Charles ya zama Sarki ne a watan Satumba na 2022 bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, wadda ta rasu tana da shekaru 96 bayan ta shafe shekaru 70 akan karagar mulki.

Labarin cutar na zuwa ne yayin da surukarsa Kate, Gimbiyar Wales, ta ke murmurewa daga tiyatar da aka yi mata a asibiti kusan makonni biyu da suka gabata.

Leave a Reply