Sani Danja, jarumi, kuma mawaƙin da ya bai wa miliyan 750 baya

0
639

Sani Musa Danja jarumi ne kuma mawaƙi, haifaffen jihar Kano. An haife shi ne a watan Afrilun 1973 kuma yana ɗaya daga cikin tsofaffi kuma fitattun jaruman fina-finan Kannywood.

KU KUMA KARANTA: Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon

Duba da nasarorin da ya samu na tsawon shekaru, ba abin mamaki ba ne cewa dukiyar Sani Danja ta kai aƙalla Naira miliyan 750. Daga cikin nasarorinsa, akwai Kamfanin Two Effects Empire wanda suka samar shida Amininsa, Yakubu Muhammad wanda shima jarumi ne.

Sani Danja tare da Yakubu Muhammad, Amincin su yakai har kaya iri ɗaya sukeyi harda yaransu duka

Sani Danja yana daga cikin jaruman Kannywood da suka auri yan’uwansu jarumai, ya auri mansurah Isah, sunada yara huɗu tare, amma sun rabu. A wasu fina finansa, yakan sako yaransu, wanda tuni yaran suma sun ƙware a harkar.

Iyalin Sani Danja

Fitowar Sani Danja masana’antar nishadantarwa ta Arewa ta faro ne tun a shekarar 1999 inda ya fito a fim ɗin ‘Dalibai.’ Tun daga nan, ya fito a fina-finai sama da 500 a Kannywood da Nollywood, wanda hakan ya sa ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan wasan da suke fitowa a film industry ɗin duka biyu.

Jarumin, a wani shiri na Nollywood

Wasu daga cikin fina-finansa na kwana – kwanan nan sun haɗa da; Ƙawayen Amarya (2018), Ana Barin Halak (2019), Amina (2021), Aisha (2022), Daughter of the river(2012), Nimbe (2019), Coming from insanity (2019), da dai sauransu.

Har ila yau, yana da shiri me dogon zango da ake kira ‘Gidan Danja’, shirin yayi suna sosai tin bayan fitowar sa.

Sani Danja Ambassador ne na wasu kamfanoni

Sani Danja yana da lambobin yabo da dama da suka haɗa da Gwarzon Jarumin Shekara, da Fitaccen Furodusan Kannywood na Shekarar 2013, da kuma gasar City People Entertainment Awards.

Leave a Reply