Sanata Uba Sani Ya Kaddamar Da Sabuwar Fadar Esu Chikun

0
346

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SANATA Uba Sani mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya kaddamar da sabuwar ginin fadar Esu Chikun da aka gina a shiyyar Kaduna ta tsakiya.

Yayin da yake gudanar da aikin katse Igiyar da ke nuna alamar kammala ginin gidan sarautar, Sanatan ya bayyana sarkin a matsayin wani abin koyi da ke nuna zaman lafiya da ci gaban al’ummar Chikun da sauran su.

Dan majalisar na Kaduna ta tsakiya ya bukaci al’ummar kananan hukumomin Jihar da ma Jihar Kaduna baki daya da su bai wa hukumomi hadin kai ta hanyar ba da kason su don tabbatar da dorewar zaman lafiya a Jihar.

Dan takarar kujerar Gwamnan Jihar a 2023, ya sake da nanata kudurinsa na daukaka jama’a a ta hanyar isar da ribar dimokuradiyya zuwa ƙofofin mabuƙata waɗanda sha’awarsu ta kasance mafi girma a cikin zuciyarsa.

Ya yi addu’ar Allah ya baiwa Esu ikon gudanar da mulkinsa cikin tsoron Allah da tausayi.

A nasa jawabin, Esu Chikun ya yaba wa gwamnatin Gwamna Nasiru El-Rufai da Sanata Uba Sani bisa kokarin da suke yi na ci gaban al’umma da Jihar baki daya.

Leave a Reply