Sana’ar Gasa Kaji Tana Da Albarka – Inji Alaramma Mai Kaji Dambatta

0
409

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

WANI fitaccen mai gasa kaji dake bakin Titin Manu Dambatta, Alaramma Mai kaji yace akwai albarka cikin sana’ar gasa kaji idan akwai kwarewa da rike gaskiya wajen mu’amulla da abokan hulda.

Ya yi wannan bayani ne a zantawar su da wakilin mu yayin da Gaskiya Tafi Kwabo ta ziyarci yankin Karamar hukumar Dambatta, inda ya kara da cewa ya dade yana wannan sana’a ta gasa kaji, sannan yace yana da abokan hulda masu tarin yawa musamman ganin cewa yana aikin gasa kaji ne a bakin kasuwar Dambatta Kuma bakin Babbar hanya.

Ya ce yana gasa kaji masu yawa Kuma masu kyau da lafiya Kuma ya dayar dasu duk da cewa ana cikin yanayi na rashin kudade a hannun al’umma, don haka baya fashin aikin gasa kaji muddin dai lafiya lau yake kuma babu wata dokar hana fita.

A kashe, Alaramma mai gasa kaji dake titin Manu Dambatta, ya yi Kira ga masu sana’ar gasa kaji da sauran sana’oi da su kara himma wajen rike gaskiya da mutuncin sana’o in su ta yadda abin zai ci gaba da kasancewa mai albarka, sannan yayi godiya ga abokan huldar sa wadanda suke tsayawa a motocin su da sauran ababen hawa suna sayen kaji domin bukukuwa ko walima.

Leave a Reply