Kyakyawar Jarumar Kannywood, Fati Abdullahi Washa ta cikin shirin wasan Hausa me dogon Zango, “Labarina” ta bayyana cewa ta shirya yin aure, amma ko wane mijin ya zama dole ya cika wasu sharuɗɗa kafin ta saurare shi.
Fati Washa mai shekaru 30, haifaffiyar Bauchi ta yi makarantar firamare da sakandare a Bauchi, daga baya ta samu shaidar NCE a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano. Daga nan ta shiga Kannywood a matsayin jarumar me tallafawa na tsawon shekaru, inda ta yi fice a fina-finan hausa da dama, kafin ta kasance cikin jarumai masu tsada. Yanzu dai ta zama babbar jaruma me daraja, furodusoshi da daraktoci a kodayaushe suna sha’awar saka doguwar jarumar ‘yar kudancin Kaduna, a finafinansu.
Neptune Prime ta jiyo cewa yanzu tana harka tare da manyan mutane da manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa, ta sami albarkatu masu yawa, daga gwala-gwalai, zuwa motoci, kuma ta gina gida ga iyayenta a cikin unguwar Kinkinau.
Fati Washa, wacce har yanzu ba ta da aure kuma a kasuwa take, ta fitar da sanarwa ta kafafen sada zumunta na zamani, cewa yanzu takai inda takeso takai a rayuwa, kuma a shirye take ta yi aure idan ta samu wanda ya cika sharuɗɗanta, wato: dole ne ya kasance attajiri, dole ne ya kasance dogo, baƙi kuma kyakkyawa.
Sannan dole ya kasance ya iya karanta alqur’ani, kuma ya haddace shi. Dole ne ya kasance mai kulawa da iya soyayya, kuma dole ne ya kasance yana mata soyayyar tsakani da Allah, kuma a karshe ya zama saurayi marar aure, kuma ba zai taɓa auren mace ta biyu ba.
Neptune Prime ta gano cewa tun bayan da ta fito da waɗannan sharudda, hakan ya rika jawo mata munanan martani a kafafen yaɗa labarai, inda wasu ke zarginta da son kai, a matsayin ta na ‘yar wasan hausa, mace mara daraja, da kuma rashin ilmin Addini dana boko. Wasu kuma na cewa aure yana buƙatar addu’a ne, ba sharaɗi mai wahala ba.