Sai ka ba ni jari na miliyan ɗari kafin In aureka -Safara’u kwana Casa’in

0
597

Daga Saleh Inuwa, Kano

Korarriyar jarumar nan ta labari me dogon zango, Kwana Casa’in, safara’u, ta gindaya wasu sharruɗa ga duk wanda ke so ya aure ta, kana ta wallafa cewa “don Allah, masoyana ku taya ni tura wannan saƙon zuwa sauran groups don jama’a su ƙara gani ko zan samu mai cika waɗannan sharruɗan.

“Zan aureka idan ka cika dukkan waɗannan sharruɗan:

Na farko dole mu yi yarjejeniya a rubuce ka sa hannu ni ma in sa, cewar bayan ka aureni za ka barni in ci gaba da sana’ata wato rawa da waƙa.

Na biyu idan ba za ka barni ba to za ka bani jarin naira miliyan 100 domin in fara zuwa Dubai ina sayo kaya ina sayarwa.

Na uku dole ka bani kyautar gida a Kaduna da Abuja da kuma motar hawa wacce ta kai darajar naira miliyan 15.

Idan ka ga za ka iya to ka ajiye min number wayarka zan kira ka.”

Tun da aka kori jarumar daga shirin kwana Casa’in, saboda bidiyo da ta saki na baɗala, saita faɗa harkar rawa da waƙoƙi na habaici da zambo dan jan hankalin jama’a.

Leave a Reply