Sai da aka kashe na’urorin ɗaukar hoto kafin a sace ɗaliban Kogi – Gwamna Ododo

0
106

Rahotanni daga jihar Kogin Najeriya na cewa an kashe duka na’urorin ɗaukan hoto a jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence University da ke jihar kafin a sace wasu ɗaliban makarantar a cewar Gwamna Usman Ododo.

A ranar Alhamis wasu ‘yan bindiga suka kutsa jami’ar wacce ke Osara suka sace ɗalibai tara cikin dare.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a ji ɗuriyar ɗaliban ko waɗanda suka sace su ba.

Ododo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ganewa idonsa jami’ar a ranar Asabar.

“Binciken da muka gudanar ya zuwa yanzu, ya nuna cewa, duka na’urorin da muka saka an kashe su, kuma wannan ba wani abu ba ne illa zagon ƙasa daga mutanen cikin gida.” Ododo ya ce.

Gwamna Ododo ya yi ƙira ga iyayen ɗaliban da su kwantar da hankulansu saboda jami’an tsaro suna bin diddigin al’amarin yana mai cewa buƙatar gwamnati a yanzu shi ne a ceto ɗaliban.

KU KUMA KARANTA:Muna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bindiga suka sace – Gwamnatin Kogi

Batun satar ɗalibai a makarantun firaimare da sakandare da ma jami’o’i a Najeriya ba baƙon abu ba ne musamman a arewaci.

‘Yan bindiga kan sace ɗalibai da dama su kutsa da su cikin daji har sai an biya kuɗin fansa kafin a sako su.

Satar mutane domin neman kuɗin fansa, babbar matsala ce a mafi akasarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Hukumomin ƙasar sun ce suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun kawo ƙarshen wannan al’amari.

Leave a Reply